Daga Imrana Abdullahi
Majalisar zartaswa ta kasa ta zabi Dokta Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa.
An yanke wannan shawarar ne a babban taron jam’iyyar na kasa (NEC) karo na 12 da aka gudanar a dakin taro na Otal din Transcorp Hilton da ke Abuja.
Ganduje ya gaji tsohon shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Adamu, wanda kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) ya kora a watan Yuni.