Home / KUNGIYOYI / Gidauniyar Aminatou Abdoulkarim “A A Charity” Ta Karrama Kwamishinar Matan Sakkwato

Gidauniyar Aminatou Abdoulkarim “A A Charity” Ta Karrama Kwamishinar Matan Sakkwato

Daga Imrana Abdullahi
A sakamakon irin kokari da jajircewa wajen ganin rayuwar Mata da Yara da sauran al’umma yasa Gidauniyar taimakawa marayu, Gajiyayyu da sauran masu bukata ta musamman ta “A A Charity” ta Karrama kwamishinar ma’aikatar da ke kula da harkokin mata ta Jihar Sakkwato, Hajiya Hadiza Ahmed Shagari.
A wajen babban taron kaddamar da shugabannin Gidauniyar da kuma raba tallafi da kayan karatu da aka rabawa yan makaranta marayu da kuma gajiyayyu a Kaduna.
An dai karbi karramawar ne a madadin kwamishinar mai kula da harkokin mata.
A wajen taron wadda ta samar da Gidauniyar baki daya Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad ta bayyana dalilin da yasa take aiwatar da ayyukan jin kai ta tabbatar da cewa ta na yin aikin ne saboda tausayi sakamakon irin yadda ya ga halin da wadansu mutane ke ciki na rayuwa.
Musamman matan da suka rasa mazajensu na cikin wani halin kakanikayi na rayuwa don haka suna tsananin bukatar taimakon al’umma.
Ga taron matan da suka cika fom da suka amfana da taimakon Gidauniyar A A Charity
Hajiya Uwani ce ta karbi karramawar a madadin kwamishinar ma’aikatar kula da harkokin mata ta Jihar Sakkwato, Hajiya Hadiza Ahmed Shagari.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.