Home / KUNGIYOYI / Gidauniyar Tunawa Da SIR AHMADU BELLO Za Ta Yi Taron Lacca Da Karrama Wasu Mutane

Gidauniyar Tunawa Da SIR AHMADU BELLO Za Ta Yi Taron Lacca Da Karrama Wasu Mutane

Mustapha Imrana Abdullahi
Gidauniyar tunawa da marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato sun bayyana cewa za su yi taron lacca da Karrama wadansu mutane karo na 7 da ake yi shekara shekara.
Manajan Daraktan gidauniyar Injiniya Abubakar Gambo Umar ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna domin yi wa manema labaran Jinjinar bangirma game da irin yadda suke yi wa gidauniyar aiki a kan harkar yayata ayyukansu, inda ya ce za a yi taron ne a ranar Asabar 29 ga watan Mayu 2021.
Kamar yadda Manajan daraktan ya ce a wajen taron karo na 7 Za’a yi laccar ne mai taken Shugabanci da kuma tafiyar da shi “cutar korona: hanyar da za a ci gaba a arewacin Nijeriya musamman game da tattalin arziki”.
A taron laccar dai ana samun halartar dimbin masana daga dukkan bangarorin ilimi domin su tattauna da nufin samo mafita game da matsalolin da ake fama da su a kowane fanni.
Za dai ayi taron laccar na ba na ne karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Plateau kuma shugaban kungiyar Gwamnonin arewacin Nijeriya Mista Simon Bako Lalong, a dakin taro da ke gidauniyar  tunawa da marigayi Sa Ahmadu Bello a ranar Asabar da misalin karfe 10 na safe, mai masaukin Baki shi ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El- Rifa’i.
Masanin harkokin tattalin arziki na duniya Farfesa Nazifi Abdullahi Darma, na jami’ar Abuja,Farfesa Ummu Jalingo, Daraktan harkokin bincike kan tattalin arziki a jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutse, Dokta Muhammad Sagagi,mataimakin shugaban kwamitin shugaban kasa da suke aikin bayar da shawara kan tattalin arzikin kasa
Da Dokta Sara Alade, tsohuwar mataimakiyar Gwamnan Bankin Nijeriya duk za su tattauna batutuwan tattalin arzikin yankin arewacin Nijeriya da hanyoyin warwaresu.
Manyan baki a wajen taron sun hada da Gwamnoni, yan majalisar tarayya, Ministoci, Sarakuna,shugabannin addini,shugabannin hukumomi da bangarorin Gwamnati da sauran wasu masu ruwa da tsaki.
Injiniya Abubakar Gambo ya kuma ce za a Karrama wadansu mutane biyu da suka bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban kasa duk za a karramawa da lambar girma.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.