Home / Kasuwanci / Za Mu Hukunta Duk Gidan Man Da Ba Su Da Kayan Kashe Gobara – Ganduje

Za Mu Hukunta Duk Gidan Man Da Ba Su Da Kayan Kashe Gobara – Ganduje

Za Mu Hukunta Duk Gidan Man Da Ba Su Da Kayan Kashe Gobara – Ganduje
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa daga yanzu duk gidan man da ba su da kayan kashe Gobara za a hukunta su.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci asibitin Murtala da ke Kano domin jajantawa mutanen da hadarin Gobarar wani gidan mai ta shafa inda suke a asibitin ana duba lafiyarsu tare da karbar magani.
Ganduje ya ce “idan da wannan mutum da ya jawo wannan Gobara ya na da horon sanin yadda ya dace ya aiwatar da aiki ta yaya zai aiwatar da irin abin da ya aikata har aka shiga matsalar da ake ciki a halin yanzu”.
“Saboda haka Gwamnati a halin yanzu za ta tabbatar da ganin an horar da wadanda za su yi wannan aiki na gidan mai kuma dole kowane gidan mai ya samar da kayan kashe Gobara domin samun saukin duk wani abin da zai faru”.
Gwamna Ganduje ya ci gaba da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta duba lafiyar wadanda lamarin hadarin ya shafa da kuma ba su magani kyauta.
Da yake tofa albarkacin bakinsa mai magana da yawun gidan man da abin ya shafa na hadarin Muhammadu Akibu, cewa ya yi za su ci gaba da taimakawa wadanda hadarin ya rutsa da su.
Idan ba a manta ba kwanan baya ne wani hadarin tankar mai ya faru a wani gidan mai a cikin garin Kano inda hadarin Gobarar ya yi sanadiyyar rasa ran mutum daya da kuma raunata wasu da dama da a yanzu suke kwance a asibitin Murtala a cikin garin Kano

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.