Gobara ta kone ginin gidan rediyon tarayyar Najeriya FRCN da ke Kaduna da yammacin ranar Lahadin nan.
Ko da yake kawo yanzu ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba amma majiyar mu ta bayyana cewa ta fara ne daga dakin bayar da wuta na Janareto kuma Dakin Janareton ya Kone kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana cewa wutar ta fara ne da misalin karfe 1:43 na rana.
“Muna fitowa daga masallaci, kwatsam sai muka ga gobara ta fito daga dakin da ke bayar da wuta na Janareto da ke a cikin gidan.”
A cewar majiyar, “Da yake a ranar Lahadi, ma’aikata kalilan ne kawai ke zuwa bakin aiki. Don haka ba mu san yadda gobarar ta tashi ba.”
Sai dai ya bayyana cewa an gayyaci jami’an kashe gobara don kashe gobarar daga yaduwa zuwa wasu gine-gine.
An tattaro cewa shiga tsakani na hukumar kashe gobara ta ceto gidan rediyon.
A ranar Juma’a ne ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Ibrahim Malagi ya je gidan rediyon domin tantance gidan rediyon inda ya yi alkawarin gudanar da gyare-gyare a gidan rediyon da kuma gidan talabijin na kasa NTA.