Home / Labarai / Gobe Za A Ba Sarkin Zazzau Sandar Mulki

Gobe Za A Ba Sarkin Zazzau Sandar Mulki

Ana Gayyatar Daukacin Jama’a Da Su Halarci Nadin Sabon Sarkin Zazzau
Mustapha Imrana Abdullahi
Babban kwamitin shirye shiryen baiwa Sabon Sarkin Zazzau mai martaba Jakada Nuhu Bamalli na 19, Sandar mulki karkashin jagorancin kwamishina ma’aikatar kananan hukumomi da masarautun gargajiya Alhaji Jafaru Sani, na gayyatar daukacin al’umma da su halarci gagarumin taron domin a cika tarihi tare da su.
Kwamishin ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun kwamishinan inda suka yi kira ga jama’a da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin a kafa wannan tarihi tare da su a mikawa Sabon Sarkin Zazzau na 19 sandar Mulki a matsayin Sarkin Zazzau na 19 wanda Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I zai mika masa a birnin Zazzau.
Za dai ayi wannan taron ne a ranar Litinin Gobe 9 ha watan Nuwamba 2020, a dandalin wasan kwallon Dawaki na Muhammadu Aminu da ke Unguwar GRA Zariya da misalin karfe 10 na safiya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa tuni aka kammala shirye shiryen gudanar da wannan taron inda daga an mikawa Sarki Sanda za a yi jerin Gwanon Dawaki a raka Sarki fadarsa cikin birnin Zazzau tare da Rakiyar Hakimai,yan majalisar Sarki Sarki sauran masu rike da sarautu da sauran dimbin jama’a tare da kade kade da bushe bushe irin na sarauta.
Sanarwar ta kuma shawarci jama’a da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya da daukakar masarautar Zazzau da al’ummarta baki daya kuma mutanen su kuma fito su yi layi tun daga Tudun Wada har zuwa Kofar doka domin nuna karramawa da cikakken goyon baya ga Sabon Sarkin.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.