Home / Labarai / GOBE ZA A CI GABA DA SAURAREN KARAR GWAMNA A KADUNA

GOBE ZA A CI GABA DA SAURAREN KARAR GWAMNA A KADUNA

Daga Imrana Abdullahi

A ci gaba da sauraren karar da dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP ya shigar  Alhaji Isa Ashiru Kudan ya na kalubalantar zaben Gwamnan da hukumar zabe ta ce Uba Sani na Jam’iyyar APC ya yi nasara.

A yau dai ranar Litinin 24 ga watan Yuli, 2023 kotun ta ci gaba da sauraren shedun da PDP keda su da ya zuwa yanzu an saurari 10 saga cikin 25 da suka ce za su Gabatarwa kotun, kamar yadda babban Lauyan Najeriya Samuel Atung SAN ya tabbatarwa da manema labarai a harabar kotun.

Lauya Samuel Atung ya ce sun Gamsu da irin yadda shari’ar ke tafiya.

Haka shima lauyan da ke tsayawa Gwamna Uba Sani, babban Lauyan Najeriya Sanusi Musa SAN ya shaidawa manema labarai cewa sun Gamsu da yadda shari’a ke tafiya har ma suna son a kammala ta.

Idan Allah ya kai mu gobe dai za a ci gaba da sauraren ci gaba da kawo shaidun da lauyan dan takarar Gwamna Isa Ashiru Kudan ke yi.

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.