Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ya marabci majalisar Masarautar Bauchi da ta kai masa gaisuwar sallah karkashin jagorancin me martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu.
Da yake jawabi, Gwamna Bala ya alakanta nasarorin da gwamnatin
sa ke samu da goyon baya da hadin kai da masu rike da masarautun gargajiya ke ba ta.
Yace rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen inganta zaman lafiya a jihar Bauchi abin yabawa ne a saboda haka ya kiraye su da su cigaba da marawa gwamnatin sa baya don sauke nauyin dake kanta na inganta rayuwar al’umar jihar.
Gwamna Bala yace cigaba na dorewa ne idan an samu kwanciyar hankali da nutsuwa a saboda haka gwamnati zata cigaba da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da tsaron lafiya da dukiyar al’umar ta.
Tun farko da yake jawabi, 5me martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu yace ziyarar ta barka da sallah zuwa fadar gwamnati na nuni da fahimta da kyakkyawuyar alakar aiki tsakanin majalisar da fannin zartaswa.
Sarkin na Bauchi yayi amfani da damar wajen yabawa gwamnan kan ayyukan jin Kai da gwamnatinsa ke gudanarwa inda ya jaddada cigaba da marawa gwamnatin baya wajen inganta rayuwar al’umar ta.
Jamilu Barau Daga Bauchi.