Home / MUKALA / ‘Ba Zamu Rufe Baki Mu Kauda Kai, Yan Arewa Suna Cikin Bala’i Don Kwadayin Mulki A 2023, Inji Gwamna Zamfara, Bello Mutawalle

‘Ba Zamu Rufe Baki Mu Kauda Kai, Yan Arewa Suna Cikin Bala’i Don Kwadayin Mulki A 2023, Inji Gwamna Zamfara, Bello Mutawalle

Lokaci ya yi da yan arewa za su dawo su yi wa kansu karatun ta natsu, a ajiye kiyayya, hassada, kwadayi da tsoro tsakanin juna a fuskanci babbar barazanar da ke kara raba makomar arewa; wato sha’anin tsaro, talauci da lallaci.
Dattawan Arewa da masu rike da madafun iko da ke ganin su ne ke rike da kambun samar da ci gaba ko makoma ga yan arewa su na da kalubalen da ke gabansu na gaya ma junansu gaskiya a kan sun kasa rike amanar da na gabansu irinsu Sardauna suka bar musu a kan makomar yan arewa da Najeriya baki daya.
Lokaci ya yi da za a zauna a yi wa juna gafara a hada kai don ganin an ceto yan kasa da ke fuskantar kalubalen tashin hankali na kisan gilla, hare-haren cin amana da kone dukiya da ake yi a Arewa ba gaira ba dalili.
Zancen makomar arewa a 2023 ba shi ne abin bayar da fiffiko ba, muhimman abu shi ne fuskantar wadanan kalubalen dake da mummuna illa ga rayuwa da dukiyar al’umma da ta sanya tabarbarewa tsaro, Ilmi da kasuwanci a kusan ko’ina na arewa, mussaman arewa maso yamma da noma ya zama tashin hankali ga jama’a.
Sai mu shugabani mun zauna tare mun amince da a zuciyoyinmu zamu sanya tsoron Allah mu yafe juna, mu aje hassada da kwadayi mulki da son rai, sa’ilin za a iya samun nasara ga lamarin da zai taimaka a kawo sauki ga wadanan matsalolin.
Akwai hatsari mai yawa wasu yan kalilan don sun ga suna da wata mafita har suyi ko oho ga bayar da hadin kai a fuskanci wannan barazana.
Lokaci ne a yanzu da ake bukatar hadin kai, aje ra’ayin ni dan jam’iyyar APC ko PDP ko APGA ko dai wacece don hadin kai a samu nasara.
Muddin wasu ko wani ke ganin, idan babu shi arewa ba za ta cimma wannan burin ba; tabbata wannan matsalar ba za ta kai karshe da sauki ba.
Duk dan Arewa yana da hakki ga ganin an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yankin, don haka lokaci ya yi da za aje ra’ayin siyasa, a manta da kabilanci na harshe ko addini a dawo ga gina kasa a samarwa jama’a kwanciyar hankali da zaman lafiya don inganta musu rayuwa da samar da makoma ta gari.
Shugabani su mayar da adalci da gaskiya tare da samarwa al’umma hanyoyin sauki ga tafiyar rayuwa da inganta musu ababen more rayuwa.
Al’umma su hada kai don baiwa gwamnati goyon baya da taimakawa jami’an tsaro a kan yaki da ta’addanci da kisan gilla  ba gaira ba dalili.
Babu wani da zai zo daga waje ya gyara mana makomarmu ko inganta mana hanyoyin rayuwa muddin bamu mayar da hankali ga wannan lamari a tsakaninmu ba.
Mai girma
Honarabul  Bello Muhammad Mutawalle,
(Shattiman Sokoto)
Gwamnan jahar Zamfara

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.