Home / Labarai / GWAMNA DAUDA LAWAL YA HALARCI TARON MAJALISAR TATTALIN ARZIKIN KASA

GWAMNA DAUDA LAWAL YA HALARCI TARON MAJALISAR TATTALIN ARZIKIN KASA

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Alhamis, ya halarci taron majalisar tattalin arzikin kasa a Abuja.

Taron majalisar tattalin arzikin kasa karo na 135 ya gudana ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Sanata  Kashim Shettima, GCON a zauren taro da ke a fadar shugaban kasa.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun SULAIMAN BALA IDRIS Babban Mataimaki na Musamman a kan harkokin hulda da kafofin yada labarai Labarai na Gwamnan Jihar Zamfara.

Taron dai ya tattauna ne kan muhimman batutuwan da suka tabarbare, kamar batun cire tallafin man fetur da kuma hanyoyin da za a bi don rage wahalhalun da jama’a ke ciki.

Bugu da kari, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kafa kwamitin da ya kunshi Gwamnoni biyar da za su gana da shugabannin kungiyar kwadago domin samun fahimtar juna kan batun cire tallafin man fetur.

 An kuma tattauna kan hanyoyin ci gaba da rabon kayan abinci a matsayin abubuwan da za su taimaka wa jama’a a duk fadin kasar nan.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.