Home / Labarai / Matsalar Tsaro: Gwamnonin Jihohin Neja Da Zamfara Sun Tattauna Da Ribadu 

Matsalar Tsaro: Gwamnonin Jihohin Neja Da Zamfara Sun Tattauna Da Ribadu 

Daga Imrana Abdullahi
Gwamnonin Zamfara da Neja, a ranar Alhamis, sun ziyarci mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.
Gwamna Dokta Dausa Lawal ya kai wannan ziyarar ne tare da gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago a ƙoƙarinsu na samar da ingantacciyar zaman lafiya a jihohinsu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya jaddada cewa gwamnonin sun yi tattaunawar ne a keɓe a ofishin Mallam Nuhu Ribadu da ke Abuja.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Lawal na cike da damuwa da matsalar tsaron da ke addabar Jihar Zamfara.
Ya ce: “Gwamna Dauda Lawal da Gwamna Mohammed Umar Bago sun ziyarci Mallam Nuhu Ribadu ne a yunkurinsu na kyautata alaƙa tsakanin jihohin da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro.
Tawagar da ta kai wa mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro Nuhu Ribadu ziyara a Ofishinsa da ke Abuja kamar yadda aka wallafa a cikin labarin
“Dawo da zaman lafiya a Jihar Zamfara shi ne abu mafi muhimmanci ga Gwamna Dauda Lawal tun bayan da ya zamo gwamnan Jihar.
“A wurin tattaunawar, gwamnonin sun samu fahimtar juna tare da Mallam Nuhu Ribadu kan muhimman batutuwa na tsaro.”

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.