Related Articles
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya yi garambawul a gwamnatinsa, sannan ya rantsar da wani sabon Kwamishina.
A Litinin ɗin nan ne Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci zaman majalisar zartarwar jihar, inda a lokacin zaman ya rantsar da wani sabon Kwamishina.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa a wannan zaman Majalisar, gwamnan ya canja wa wasu Kwamishinoni wuraren aiki.
Sanarwar ta ce, an naɗa sabon Kwamishinan, Kasimu Sani Kaura ne don ya maye girbin Mannir Muazu Haidara, wanda ya ajiye aiki, kuma aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.
Gwamna Lawal ya bayyana wa Majalisar cewa dacewa ce ta sa aka zaɓo Kasimu Sani Kaura don ya wakilci al’ummar Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda a Majalisar, wanda kuma ya kasance mutum ne jajirtacce game da ci gaban al’ummarsa, da ma jihar baki ɗaya.
Gwamnan ya ce, “Wannan naɗi, wata alamar tabbaci ce ta gwamnatin nan na zaƙulo jajirtattun mutanen da za su bayar da gagarumar gudumawa wajen inganta rayuwar al’umma da ci gaban jihar Zamfara.
“Ina mai yin kira ga sabon Kwamishinan kan ya bayar da rayuwarsa wajen yi wa al’ummar sa hidima. A matsayin sa na mamba a harkar ceto jihar Zamfara, ba ni da shakkun irin gagarumar gudumawar da zai bayar don amfanin jama’a.
“Mai girma Kwamishina, ina taya ka murnar wannan kira da aka yi maka don ka yi wa al’umma hidama. Ina maka, tare da dukkan mu fatan tsarewar Allah. Ina mai kira gare ka da ka kasance kana aiki kafaɗa da kafaɗa tare da sauran Kwamishinoni, da kuma ma’aikatan ma’aikatarka.
Gwamnan ya ce, ya lura da yadda dukkan muƙarrabansa ke gudanar da ayyukansu, wanda hakan ne ta sa ya yi wasu ‘yan canje-canje. “Don ganin mun samu nasarar sauke nauyin da ke kanmu, ina ganin akwai buƙatuwar yin wasu ‘yan canje-canje a gwamnatina.”
“Wannan sabon Kwamishina, Kasimu Sani Kaura, zai kula da ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa, inda ya maye gurbin Hon. Mahmud Mohammed Abdullahi, Wanda aka mayar da shi mai kula da ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu.
“Hon. Nasiru Ibrahim Zurmi kuma ya koma Kwamishina a ma’aikatar kula da birane, inda ya maye gurbin Hon. Kabiru Moyi, wanda ya koma. Ma’aikatar sanya ido da aiwatar da ayyuka.
“Bugu da ƙari, an canja Dr. Nafisa Muhammad zuwa ma’aikatar lafiya, inda ta maye gurbin Dr. Aisha M. Za Anka, wacce ta koma Kwamishina a ma’aikatar kula da mata da inganta jin daɗin jama’a.
“Za a kammala duk wasu shirye-shiryen miƙa shugabancin a tsakanin kwanaki bakwai. Ina so in ƙara tunatar da ku cewa zan ci gaba da sanya ido da yadda kuke gudanarwa, tare da auna ayyukanku, domin muna fuskantar rabin wa’adinmu a ofis. Mu yi amfani da wannan dama wajen jajircewa da sadaukarwa wajen yi wa jihar mu ta Zamfara hidima.”