Home / Labarai / Gwamna Dauda Lawal Ya Yabawa Shirin SDG Na Samar Da Hasken Sola A Jihar Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Yabawa Shirin SDG Na Samar Da Hasken Sola A Jihar Zamfara

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Laraba, ya sake sabunta kudirin gwamnatinsa na samar da ci gaba mai dorewa, (SDG) matasa.

Tawagar matasan SDG ta je jihar Zamfara ne domin yi wa gwamnan bayani kan shirin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga wasu zababbun manyan makarantu a fadin Najeriya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, kungiyar matasan SDG ta zabi Zamfara a cikin jihohi 12 da za su aiwatar da aikin samar da hasken rana.

Ya ce: “Gwamna Dauda Lawal, yayin da yake karbar tawagar Matasan SDG, ya nanata shirin gwamnatinsa na bayar da tallafin da suka dace.

“Ya bayyana jin dadinsa da zaben Zamfara a cikin jihohi 12 da za su ci gajiyar girka wutar lantarki a fadin Najeriya.

“Aikin SDG na matasa yana da nufin samar da wutar lantarki mai karfin KV 100 ga Kwalejin Ilimi ta Maru sannan kuma zai horas da matasa sama da 50 a kan girka da kula da wutar mai amfani da hasken rana.

Tawagar ta bayyana cewa gwamnatin Saudiyya da BME Korean ne suka dauki nauyin wannan aikin a karkashin kungiyar agajin ci gaban kasashen waje (ODA) kuma hedkwatar matasa ta SDG a Koriya ta Kudu ne suka dauki nauyin aikin.

“Gwamna Dauda Lawal ya ci gaba da cewa da gangan ya zabi kwalejin ilimi ta Maru domin gudanar da aikin gwajin na’urar samar da hasken rana a wani bangare na kudirinsa na sake fasalin fannin ilimi a jihar Zamfara.

“Tawagar ta ce ziyarar za ta bayar da dama ga jihar wajen ciyar da matasa gaba ta fuskar noman fasaha;  damar tallafin karatu;  Kula da Lafiya na Farko;  Ci gaban Wasanni;  Ilimin yara Mata da Fasahar Sadarwa.

Tawagar matasan SDG kenan da suka kawo wa Gwamnan Jihar Zamfara ziyara

“Tawagar matasan SDG ta kunshi manyan jami’an gwamnati daga Abuja karkashin jagorancin wakilin shiyyar Najeriya da Afirka, Mista Uzoh Ifeanyi C.”

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.