Daga Imrana Abdullahi
A kokarinsa na ganin an ceto Jihar Zamfara, daga halin da take ciki gwamna Dokta Dauda Lawal ya gana da jakadiyar tarayyar Turai a Najeriya, Samuela Isopi a ofishinta, a wani yunkuri na neman karin tallafi ga jihar ta bangarori da dama.
Bauanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Nuhu Salihu Anka, Darakta Janar, na Gwamna mai kula da Kafofin watsa labarai da Sadarwa da aka raba wa manema labarai
Gwamna Dauda wanda ya bayyanawa E. U irin halin da Jihar Zamfara ke ciki a halin yanzu musamman a fannin ilimi, tsaro, lafiya, tattalin arziki, karfafa matasa da dai sauran su, ya ce jihar na matukar bukatar alaka mai karfi da su domin samar da gyara a jihar.
Ya kuma yi nuni da cewa, jihar na bukatar tallafi daga kungiyar tarayyar turai musamman kan harkokin tsaro wanda ya zama wajibi ga duk wani ci gaba, da kuma tallafi a wasu bangarorin da suka hada da Ilimi musamman ilimin yaya mata, kiwon lafiya, samar da ruwan sha, raya karkara da birane.
Sauran bangarorin da ke bukatar tallafi kamar yadda ya ambata, su ne, samun kwarewa don ci gaba da samar da ayyukan yi wanda hakan zai taimaka wajen rage ayyukan aikata laifuka a jihar wanda kungiyar Tarayyar Turai ta ba da fifiko a ayyukanta na shiga tsakani.
Mai martaba ya kuma yi kira ga kungiyar EU da ta ba da gudummawa ta musamman don farfado da fannin kiwon lafiya ta hanyar samar da kayan aiki na zamani, kayan aiki, ma’aikata da sauran kayayyakin da ake bukata domin samun ingantaccen tsarin kiwon lafiya musamman cibiyoyin kiwon lafiya na farko.
Gwamnan wanda ya kuma bayyanawa jakadan wasu tsare-tsare na gwamnatinsa na kawo sauyi, ya ce, ya zuwa yanzu ya samu damar rage kudaden gudanar da harkokin mulki a jihar, ta hanyar rage yawan ma’aikatu daga ashirin da takwas (28) zuwa ma’aikatu goma sha shida.
wanda ya samu kwararrun jami’ai masu dimbin kwarewa da gaskiya a aikin gwamnati, ya kuma kara da cewa ya kuma rage yawan sakatarorin dindindin da nufin rage yawan ma’aikatan gwamnati da rage tsadar kayayyaki da tabbatar da ingantaccen tsarin mulki.
Tun da farko, Ambasada Samuela Issopi, wadda ta jagoranci tawagar kungiyar ta EU a ziyarar ban girma, ya ce akwai bukatar samar da hadin kai tare da Najeriya kan harkokin tsaro musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Ambasada Issopi ta ce kungiyar E.U za ta hada hannu da gwamnatin Jihar Zamfara musamman kan sauyin yanayi, bunkasa ilimi, shiga tsakani wajen gudanar da shugabanci na gari, ‘yancin mata, aiwatar da hakkin yara da dai sauransu.
Ta taya gwamna Dauda Lawal murnar nasarar lashe zaben, inda ta ce kungiyar tarayyar Turai ta shirya kai ziyara wasu jihohi kuma Jihar Zamfara na cikin jihohin da za a fara ziyarta.