Home / News / Gwamna El- Rufa’i Cikakken Mai Kishin Talakawa Ne – Dakta Shinkafi

Gwamna El- Rufa’i Cikakken Mai Kishin Talakawa Ne – Dakta Shinkafi

Daga Abdullahi Dan Kaduna
Wani mai rajin kare hakkin bil’adama da ke garin Kaduna Dakta Suleiman Aliyu Shinkafi ya bayyana Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, a matsayin Gwarzo cikakken dan kishin kasa mai kaunar ci gaban Talakawa a koda yaushe.
Kaduna
Ga irin ayyukan Malam a Kaduna
Dakta Suleiman Aliyu Shinkafi ya bayyana hakan ne a garin kaduna inda ya ce “Wallahi Gwamnan kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i duk ya fi sauran Gwamnonin baki daya saboda idan ya tsaya a kan batun gaskiya ba wata sauran magana”.
Aikinmalam
Ga iron aikin hanyar da Malam Nasiru Ahmad ke aiwatarwa
Ya ci gaba da cewa ka duba irin ayyukan da mutumin nan yake yi su ake cewa ci gaban al’umma.
“Na bi ta wajen Ofishin KASTELEA aikin hanyar da aka yi hakika an yi mai kyau kamar ba a kaduna mutum yake ba idan ya bi ta wurin”.
Ga aikin titin Sakkwato cikin garin kaduna
Ya kara da cewa da zarar ya samu ya kammala ayyukan da ya tasa a gaba shi kenan ya bude wa dukkan jama’a idanu nan gaba kowa zai zama Gwamna a Kaduna sai ya tashi tsaye sosai ya aiwatar da ayyukan ci gaban jama’a.Saboda haka ni da an ce in kawo mutum mai kishin al’umma Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i Gwamnan kaduna kawai zan nuna ba sauran wata magana.
Dakta shinkafi ya ce ga ayyukan manya manyan tituna ana ta yi a ko’ina duk domin jama’a wannan shi ne aikin mutane.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.