Home / Labarai / Gwamna El-Rufai Ya Yi Tir Da Harin A Kauru

Gwamna El-Rufai Ya Yi Tir Da Harin A Kauru

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamna Malam Nasiru El- Rufa’I ya yi Tir da Allah wadai da kakkausar murya da harin da aka kai a ranar Litinin a wasu kauyuka a karamar hukumar Kauru.
Kauyukan sun hada da Unguwar Magaji, Kigam,Kisico da Kikobo duk a cikin karamar hukumar Kauru a Jihar Kaduna.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai da ke dauke da sa hannun kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan.
Kamar yadda rahoton da ya fito daga hedikwatar tsaron Najeriya a bangaren “Operation Safe Haven” cewa wadansu mahara sun kai wa wadannan kauyuka hari da sanyin safiyar ranar Litinin, inda nan take suka bar mutane shida matattu. Wadanda aka kashe din sun hada da :
1- Joseph Maza
2- Timvan Cibi Ciwo
3- Monday Titus
4- Asabe Magani
5- Laraba Dan ladi
6- Yosi Dan ladi
Lokacin da jami’an tsaro suka samu labarin faruwar lamarin nan da nan suka kai dauki wurin da abin ya faru kuma dole suka Sanya maharan suka tsere .
Kari a kan abin da ya faru shi ne an samu gidaje 8,dakunan ciyawa 6, Babur na hawa 1, da kuma na’urar Janareto duk an Kone su baki daya, an kuma lalata masara a lokacin da aka kai harin.
Gwamna El- Rufa’I ya yi Tir da wannan harin abin da ya bayyana da kokarin Sanya rayukan jama’a cikin wani hali. Ya yi addu’ar neman Gafara da wadanda suka mutu da kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalai da yan uwan wadanda suka rasa rayukansu.
Sai ya bukaci jami’an tsaro da su gudanar da bincike a baki dayan wurin da lamarin ya faru.
Ya zuwa yanzu ana can ana gudanar da bincike a gurin baki daya kuma  Gwamnati za ta ci gaba da gayawa jama’a abin da ke faruwa a karamar hukumar Kauru.
Sojoji da sauran jami’an tsaro na aiki tare da Gwamnati su na yin aiki da Gwamnatin Jihar Filato domin a tabbatar da al’amura sun inganta tsakanin karamar hukumar Kauru da mutanen karamar hukumar Bassa da suke a Jihar Filato.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.