Home / Labarai / Gwamna El-Rufa’I Zai Yi Amfani Da Jirgin Sama Domin Raba Magunguna

Gwamna El-Rufa’I Zai Yi Amfani Da Jirgin Sama Domin Raba Magunguna

Gwamna El-Rufa’I Zai Yi Amfani Da Jirgin Sama Domin Raba Magunguna
 Imrana Abdullahi
A kokarin Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufai na ganin jama’ar Jihar sun samu ingantaccen magani domin kula da lafiyarsu a yanzu haka shahararren Malamin ya sanya hannu a wata yarjejeniya da wani kamfani mai suna Zipline a wani tsari na raba magani a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya ta hanyar amfani da kananan jirage masu sarrafa kawunansu (drones).
A jawabinsa, Gwamna El-Rufai ya ce wannan kamfani na Zipline da ke Kasar Amurka wanda ke da reshe a Kasar Ghana ya zabi Jihar Kaduna ne don ganin irin yadda jihar ta dauki sha’anin kiwon lafiya da muhimmanci, kuma Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I ya amince da wannan tsarin ne domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Gwamnan ya kara da cewa, “ wannan tsari zai taimaka mana wurin rarraba magani da alluran riga-kafi zuwa duk lunguna da sakunan da ke jihar nan musamman inda muke fama da matsalolin tsaro kamar Birnin Gwari. Sannan wannan tsarin zai taimaka mana wurin samar da ayyukan yi ga matasanmu tunda a nan Kaduna za su rika kera wadannan jirage masu sarrafa kawunansu”.

About andiya

Check Also

Our Mandate Is To Organise Congresses, Says Labour Party Transition Committee Chairman, Umar

  Former president of the Nigerian Labour Congress, NLC, and Transition Committee chairman of the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.