Home / KUNGIYOYI / Kungiyar AYDA Ta Koka Da Matsalar Tsaron Yankin Ke Fama Da Shi

Kungiyar AYDA Ta Koka Da Matsalar Tsaron Yankin Ke Fama Da Shi

Kungiyar Matasan  Ta Koka Da Matsalar Tsaron Yankin Ke Fama Da Shi
 Imrana Abdullahi
Kungiyar ci gaban Matasan yankin arewacin Nijeriya Arewa Youth Development Association (AYDA) sun yi kira ga daukacin Gwamnonin arewacin kasar 19 da su hada kai da nufin magance matsalar tsaron da ke addabar yankin.
Shugaban kungiyar na kasa kwamared Imrana Nass ne ya yi wannan kiran inda ya bukaci Gwamnonin su dakatar da matsalar baki dayan ta.
Ya ce yankin arewacin Nijeriya a matsayinsa na wurin da babu ci gaban da ya dace a cikinsa, wanda hakan yasa al’amura ke kara sukurkucewa da mutane ke fama da matsalar satar Mutane,yan bindiga,satar dabbobi da kuma matsalar Kunar bakin wake da ya zamowa Jihar Borno wata barazana.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai da ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Imrana Nass (shugaban talakawa).
Imrana Nass ya kara da cewa matsalar tsaron da ake fuskanta a halin yanzu na kawowa yankin matsalar da ke addabar kowa.
 Shugaban kungiyar na kasa ya ce Gwamnatin da ke ci a yanzu ta bayar da dukkan damar da ya dace yankin ya samu ta hanyar nada yan asalin yankin a muhimman mukamai, amma kuma mutanen yankin na fama da matsalar yan Ta’adda Ta’adda sauran nau’in matsalar tsaro.
Kamar yadda takardar da aka rabawa manema labarai ta bayyana cewa irin matsalar tsaron da yankin ke fama da ita wata alamace da ke barazanar Jefa tsoro a zukatan jama’a da ya haifarwa mutane da suka hada da baki shiga cikin wani yanayin rashin tabbas.
Shugaban kungiyar na kasa  Imrana Nass ( shugaban talakawa) ya bayyana yanayin da ake ciki a matsayin abin damuwa da ke haifar wa yankin Arewa karuwar matsala.
“Hakika muna bukatar matukar neman dauki daga hukumomi, domin irin yadda ake kashe jama’a na bukatar a Dakatar Dakatar shi, saboda mutane sun fara dawowa daga rakiyar Gwamnatin da suka zaba”. Inji Imrana Nass.
“Muma yan Nijeriya ne kamar yadda mutanen sauran yankunan suka kasance yan Nijeriya, don haka rayukanmu da dukiyarmu duk abubuwan duba wa ne da ke da muhimmanci da ya dace a kula da su ta kowace hanya domin suna bukatar kulawa, kuma muna bukatar samun zaman lafiya da karuwar arziki domin ci gaban da kowa ke bukatar samu”.
” Gwamnati ya dace ta dauki matakin maganin matsalolin da suke addabar yankin Arewa ta hanyar samar da muhimman abubuwan ci gaban rayuwa da suka hada da samar da kayan kula da kiwon lafiya,kayan karatu a makarantu, ingantaccen ruwan sha da hanyoyi masu kyau a matsayin ciyar da kasa gaba wanda hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a Nijeriya”, inji Imrana.
Ya kuma yabawa shugaba Muhammadu Buhari a game da nadin sababbin shugabannin hukumomin tsaron Nijeriya da ya yi, inda an karar da su a kan bukatar da ke akwai su dauki matakan da suka dace domin magance matsalar tsaron da ake fama da shi.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.