Home / Labarai / Gwamna Ganduje Ya Rabawa Masu Nakasa Kekuna 52

Gwamna Ganduje Ya Rabawa Masu Nakasa Kekuna 52

Gwamna Ganduje Ya Rabawa Masu Nakasa Kekuna 52
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin masu fama da Nakasa a cikin al’umma sun samu saukin rayuwa kamar kowa Gwamnan Jihar Kano Alhaji Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya rabawa masu fama da nakasar rashin kafa Kekunan da za su taimaka masu guda 52.
Gwamnan ya dai bayar da wadannan Kekunan ne ta hanyar gidauniyarsa ta Ganduje a wajen wani gagarumin taro a Kano
Malam Rabi’u Garko shugaban bangaren lafiya na Gidauniyar  Ganduje kuma wakilin Gwamna a wajen taron rabon Kekuna 52 ha masu bukata.
ya ce a matsayinsa na shugaban korar cutar shan inna a Kano suna kiran wadannan mutane 52 da cewa wadanda suka rayu ne duk da cutar shan inna ta kamasu.
Garko ya kuma ce wanann daya ne daga cikin irin ayyukan da gidauniyar Ganduje ke yi da suka hada da yi wa masu fama da ciwon idanu aiki kyauta domin su samu lafiya kar kowa.
Ya ce wannan bayar da Kekunan Nakasassu guda 52 daya ne daga cikin irin ayyukan da Gidauniyar Ganduje ke yi domin Tallafawa mutane masu bukata.
Yau shekarun gidauniyar Ganduje shekaru 27 ana gudanar da ayyukan taimakon al’umma.
Garko ya ci gaba da cewa suna fata kamar yadda duniyar Gwamna Ganduje ta yi kyau lahirarsa ma ta yi kyau saboda irin kyawawan ayyukan da yake yi domin inganta rayuwar al’umma.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.