Daga Imrana Abdullahi
Gwamna Dauda Lawal, a ranar litinin, ya kara kaimi ga karin dakarun soji da shiga tsakani domin magance matsalar rashin tsaro a Jihar Zamfara.
Gwamna Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce babban hafsan sojin ya je rangadin aiki a shiyyar Arewa maso Yamma ne.
Ya kara da cewa shugaban ya tattauna da gwamnan kan yadda za a inganta hadin gwiwa da samar da hanyoyin yaki da matsalar ‘yan fashi a jihar.
“Shugaban hafsan soji, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya kai ziyarar aiki a yankin Arewa maso Yamma. Yayin da yake jihar Zamfara ya yi ganawar sirri da Gwamna Lawal inda aka tattauna muhimman batutuwan tsaro.
“Gwamnan da Hafsan Hafsoshin Sojoji sun tsara dabarun da za su inganta ayyukan soji don dawo da cikakken zaman lafiya a Jihar.
“Ziyarar da Shugaban Rundunar Sojin ya kai ta nuna alamar jajircewa wajen magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita. Hakan kuma zai kara kwarin gwiwar sojojin da ke fagen fama.
“Laftanar Janar Lagbaja ya tabbatar wa Gwamnan cewa nan da ‘yan makonni za a kai wani mummunan farmaki a jihar Zamfara.”