Home / News / Gwamna Malam Nasiru El- Rufa’i Adalin Mutum Ne – Mamadi

Gwamna Malam Nasiru El- Rufa’i Adalin Mutum Ne – Mamadi

Mustapha Imrana Abdullahi
Honarabul  Muhammad Abubakar Mamadi daga karamar hukumar Igabi, ya bayyana Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i da cewa mutum ne da ke son yi wa kowa adalci domin kwalliya ta biya kudin Sabulu.
Muhammad Abubakar Mamadi ya bayyana hakan ne lokacin da yake yi wa yayan jam’iyyar APC jawabi a wajen wani babban taron da ya kira a Kaduna.
Abubakar Mamadi, ya ce babban dalilin da ya sa muka kira wannan taron shi ne a gaya wa kowa irin halin da ake ciki game da lamarin APC a karamar hukumar Igabi, shi ne
” Mai girma Gwamna mai adalci Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, ya ce kowa ce karamar hukuma ta tabbatar an yi wa dukkan dan jam’iyya adalci a cikin APC, wato kowa ya bi ka’idar da jam’iyya ta shimfida ba maganar son rai a cikin harkokin jam’iyya, don haka muka ga ya dace a tara jama’a domin duk mai hakki a ba shi hakkinsa kamar yadda doka da ka’ida suka tanadar”.
Don haka ina mai tabbatar maku cewa Gwamna ya bayar da umarnin cewa aje ayi aiki da dukkan ka’idojin da doka ta tanada ta yadda za a yi wa kowa adalci a dukkan al’amura.
A wajen taron masu ruwa da tsakin akwai tsohon dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Igabi Barista Ibrahim Bello Rigachikun kuma duk sun shaidawa taron irin aniyar maigirma Gwamnan Jihar Kaduna na yi wa kowa adalci domin samun nasarar da ake bukata.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.