Home / Labarai / Gwamna Masari Ya Nada Mutumin Da Ya Dace – Sajan Haruna

Gwamna Masari Ya Nada Mutumin Da Ya Dace – Sajan Haruna

Daga Wakilinmu
Gwamna Masari Ya Nada Mutumin Da Ya Dace – Sajan Haruna
Sakamakon nadin da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi wa Bature Umar a matsayin sabon sakatarensa ya sa al’umma ke yin jinjina da farin ciki a game da wannan nadin.
Kamar dai yadda bayanai suka gabata a wata sanarwa cewa gwamna Aminu Bello Masari ya nada sabon PPS, wato sakatarensa da zai yi aiki a ofishin Gwamnan tare da shi.
 Alhaji Aminu Bello masari Dallatun Katsina matawallen Hausa an bayyana matsayin da ya ba Alhaji Bature Umar Masari na PPS na gidan Gwamnatin jahar katsina a makon daya gabata a matsayin abin da ya dace a lokacin da ya dace domin ci gaban jama’ar Jihar katsina arewaci da kasa baki daya.
Alhaji Haruna Muhammad shugaban kungiyar yan asalin karamar hukumar Kafur mazauna Funtuwa ne ya yi wannan yabon da jinjina ga Gwamna Aminu Bello Masari.
Alhaji Haruna Muhammad da aka fi Sani da (Sagent) wanda kuma shi ne shugaban kungiyar direbobi ta kasa NURTW shiyyar Arewa maso Yamma, inda ya tabbatarwa manema labarai cewa wannan matsayi da aka ba Bature Umar Masari ya cancanci hakan bisa la’akari da nagarta da kuma kwazon aiki na wanda aka nada a matsayin sakataren Gwamna na kashin kansa da zai yi aiki a gidan Gwamnati tare da Gwamnan.
 Hakika Gwamna Masari ya yi Dogon nazari kafin ya bayar da wannan mukami kuma ya mikashi ga mutumin da ya dace wato Alhaji Bature Umar Masari da ya san hidimar jama’a ya dade da sanin makamar aiki tun daga matakin karamar hukuma zuwa har ga Gwamnatin tarayya.
“Wannan mukamin ya canchanci wanda a kaba shi yace Gwamna Alhaji Aminu Bello masari ya pyi dogon nazari wajen bayar da wannan mukami kuma ya yishi a dai dai lokacin daya dace”.
Ya ci gaba da cewar “na san Gwamna tun muna yara kanana saboda tare muka taso da shi ya san halayyarsa mutum ne mai kwazo da hakuri da sanin yakamata mai yafiya a dukkan lamuransa”, inji Sajen Haruna mai ritaya.
“Hakika tun muna yara alamomi da yawa sun nuna cewar,Maigirma Gwamna Alhaji Aminu masari shugaba ne kuma mara son abin duniya sannan shi mai tausayi ne kowa ya san hakan don haka wannan mutsayin ba wai ‘yan asalin karamar hukumar Kafur kadai suka samu ba Al’ummar jihar ne baki daya”.
 Shugaban kungiyar yan asalin karamar hukumar Kafur  ya ce wanda a kaba mukamin Alhaji Bature Umar Masari mutum ne haziki mara kasala kuma jajirtaccen mutum mai amana wanda zai ci gaba da hada kan ma’aikatan gidan Gwamnatin da Al’umma jahar baki daya gaba da rike amanar Gwamnatin jihar katsina da ta maigirma Gwamnan Katsina”.
 Alhaji Haruna Muhammad ya ce irin mukaman da Alhaji Bature Umar Masari ya rike su na da yawa kuma ya na da gogewar aiki da iya hulda da jama’a  daga nan kungiyar ta yabawa Gwamna Alhaji Aminu Bello kuma ta taya Dan’uwansa Bature Umar murnar mukamin daya samu sannan kungiyar ta yi kira gare shi daya kara rike amanar maigirma Gwamnan Alhaji Aminu Bello da ta jama’ar jihar baki daya.
kungiyar ta yabawa Gwamnan jihar wajen kokarinsa na gudanar da manyan aiyuka a dukkan fadin jihar da irin kokarin  da Gwamnati ke yi wajen kawo karshen ta’addancin da ke damun wadansu yankunan jihar da yadda Gwamnatin jihar ta gabatar da manyan aiyuka a yankin karaduwa da sauran sassan Jihar domin samun jin dadi da walwalar al’umma.
Sai Sajen Haruna, ya yi kira ga daukacin jama’a da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnatin Dallatun Katsina, Matawallen hausa ya samu sukunin ci gaba da aiwatar da aikin raya kasa da al’umma baki daya.
 Shugaban kungiyar ya yi kira ga dukkan Al’ummar jihar da su ci gaba da addu’o’i ga wannan Gwamnatin mai albarka kuma mutane su guji ya da jita jita da fatan Allah ya kawo karshen wannan ta’addancin daya addabi wadansu sassan jihohin kasar nan da kuma wadansu yankunan kananan hukumomin jahar katsina.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.