Home / News / Gwamna Matawalle Ya Gamsu Da Zaben APC A Maradun

Gwamna Matawalle Ya Gamsu Da Zaben APC A Maradun

Mustapha Imrana Abdullahi
Sakamakon irin yadda aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC a matakin kananan hukumomi cikin kwanciyar hankali da lumana tare da da’a, biyayya ya sa Gwamna Matawalle farin ciki da murna bisa nasarar da aka samu.
Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Bello Muhammad Matawalle MON (Shatiman Sakkwato) ya yabawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC game da irin nasarar da aka samu wajen gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a wajen babban taron jam’iyya da aka yi domin zaben shugabannin APC na karamar hukumar Maradun wanda aka yi a dakin taro na A’ishatu Multi – Purpose da ke garin Maradun.
Ya ce matakin da shugabannin jam’iyyar tare da mabiyansu da kuma masu ruwa da tsaki  suka dauka na ganin an yi komai tare da fahimta, hadin kai cikin kwanciyar hankali da lumana a matsayin yan uwan Juna wanda hakan ya Sanya jam’iyyar ta zama abin da kowa ke bukata.
Kamar yadda ya ce, sakamakon zaben shugabannin jam’iyyar ta hanyar dai- daitawa da kuma yarjejeniya da ya tabbatar da hadin kai wani abu ne da ba a taba yinsa ba a tarihin Jihar Zamfara.
Matawallen Maradun ya bayyana farin cikinsa da ganin shugabannin da suka hada da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Ahmed Sani Yarima, tsofaffin mataimakan Gwamna, yan majalisu na da da na yanzu da suke a matakin jiha da kasa baki daya da sauran masu ruwa da tsaki da a koda yaushe suke karkashin Inuwa daya ta yan uwantaka da soyayyar juna suka hadu a cikin Mullinsa karkashin APC, sakamakon hakan a yanzu Jihar ta kama hanyar samun ci gaban da kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Gwamnan ya ci gaba da cewa tsarin siyasar da yake aiki da shi a halin yanzu babu batanci ko yaudarar Juna balantana wani ko wasu suga kamar an ware su a can gefe guda, saboda ana yin aiki ne tukuru da hangen nesa domin a cimma nasarar da kowa ke bukatar samu ta hanyar hadin kai da taimakon Juna wanda hakan zai taimaka wajen dawo da taaron lafiya da dukiyar jama’a da kuma samawa jama’a abin yi musamman ma matasa.
Barden na kasar Hausa, ya bayyana matukar jin dadinsa da ganin irin yadda yayan jam’iyyar suka fito, sakamakon hakan Gwamnan ya yi masu godiya musamman ga masu zaben shugabannin na matakin kananan hukumomi wanda sakamakon aikinsu aka samu nasarar zaben karbabbun shugabanni.
Gwamnan ya kuma shawarcesu da su ci gaba da zama masu biyayya da taimakon Gwamnatinsa domin hakan zai bashi damar cika alkawarin da ya yi wa jama’a
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban gudanar da zaben da uwar jam’iyya ta kasa ta aiko Jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Ibrahim Masari, ya shaidawa mahalarta taron da suka hada da masu zaben shugabannin cewa sun zo Jubar ne domin cika irin tanajin da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin jam’iyya.
Masari ya ce sun samar da takardun tsayawa takara ga dukkan wanda ke son tsayawa takara kuma sun tantance su domin yin zaben.
Ya ci gaba da cewa a karamar hukumar Maradun sun Gamsu da irin yadda abin ya gudana domin an samu shugabanni ta hanyar dai- daitawa da Juna a tsakanin yan takara, wanda kuma hakan tsarin mulkin jam’iyya ya amince da hakan kuma dukkan mutane sun amince wanda hakan ya Sanya aikinsu ya zo cikin sauki.
Ya ce saboda hakan ne ya sa suka bayyana yan takarar kuma dukkan masu zaben suka bayyana amincewa da su
Sai ya yabawa shugabanni da magoya bayan jam’iyyar da kuma Gwamnatin Jiha karkashin jagorancin Gwamna Bello Muhammad Matawalle sai ya shawarci yayan jam’iyyar da su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya tare da yin biyayya ga kundin tsarin mulkin.
A karshen zaben, Alhaji Yakubu Gado ne aka zaba matsayin shugaba, Malam Yunusa Magaji a matsayin Sakatare tare da sauran shugabanni.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamnan farar hula na farko Sanata Ahmad Sani Yarima Bakura,Ambasada Bashir Yuguda Gusau, shigaban majalisar dokokin Jihar Zamfara honarabul Nasiru Mu’azu Magarya, Sanata Hassan Muhammad Nasiha,Sanata Lawal Hassan Dan – iya, tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Malam Ibrahim Wakalla Muhammad da kuma Honarabul Muktar Ahmad Anka,Honarabul Aminu Sani Jaji,sai shugaban majalisar dokokin Jihar Zamfara da ya sauka kwanan nan Honarabul Sanusi Garba Rikiji da Honarabul Sani Andullahi Shinkafi.
Sauran sun hada da Ambasada Abubakar Chika Bunu, da yan majalisun jiha da na tarayya da sauran shugabannin jam’iyya da magoya bayansu.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.