Home / Labarai / Gwamna Matawalle Zai Gabatar Da Jawabi A Wajen Taron Matasa A Kan Harkar Tsaro

Gwamna Matawalle Zai Gabatar Da Jawabi A Wajen Taron Matasa A Kan Harkar Tsaro

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Mutawalle zai gabatar da kasida a game da kalubalen  tsaro, ci gaban Siyasa yadda lamarin ya shafi arewacin Nijeriya.
Zai gabatar da jawabin ne a babban taron marubuta a kafafen yada labarai na arewacin Najeriya da za a yi a ranar Lahadi 25 ga watan Yuli, 2021.
A cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gamayyar, Haidar Hashim Kano, da aka fitar ranar 24 ga watan Yuli, 2021, ta ce an shirya yin taron ne da misalin karfe 10 na safiya.
“Gwamnan Jihar Zamfara ne zai gabatar da takarda a wajen taron mai taken, “Yaki da matsalar yan bindiga a arewacin Najeriya: Kalubale da kuma mafita”, in ji takardar sanarwar.
Kamar yadda takardar sanarwar ta sanar sama da matasa dubu daya “1000” ne za su halarci taron wanda akasarinsu mambobin wannan gamayya ne daga Jihohin arewa 19 da suka hada da Abuja duk ana saran za su halarci taron na shekara.
“Taron dai zai samu halartar Gwamnonin Zamfara da Kaduna, Kakakin majalisar dokokin jiha, yan majalisun tarayya,Sarkin Zazzau, shugabannin harkokin tsaro da suka yi ritaya,yan kasuwa da sauran muhimman mutane daga fadin kasar baki daya”, kamar yadda aka sanar.
Kungiyar Marubutan a kafofin yada labarai na Arewa an samar da ita ne domin fadakarwa a kan batun samar da zaman lafiya, hadin kai da kuma fahimtar Juna a tsakanin yan Najeriya.
Kuma kungiya ce ta hadin Gwiwa daga mambobi daban daban na matsa da suka kasance alkawari masu amfani da dandalin Sada zumunta a yanar Gizo, da kuma yan jarida da masu yin sharhi a kafafen yada labarai da suka kasance masu bukatar harkokin siyasa, ci gaban kasa daga yankin arewacin Najeriya.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.