Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Tahir Gambo Abubakar, daga mazabar dan majalisar Jiha ta Doka/ Gabasawa, ya yabawa Balaraben Gwamna Sanata Uba Sani, bisa kokari da irin adalcin da yake yi wa al’ummarsa da yake jagoranta musamman sakamakon irin ayyukan da yake shimfidawa jama’a cikin birane da karkarun Jihar Kaduna da kowa ke ganinsu a kasa ana aiwatarwa wadansu ma tuni an kammala jama’a na amfanar su.
Honarabul Tahir Gambo Abubakar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna, domin jin ta bakinsa game da takarar dan majalisa da yake yi a halin yanzu.

Tahir Gambo, ya ci gaba da bayanin cewa ya zama dole a jinjinawa Gwamna Uba Sani saboda irin kokarin da yake yi wajen kammala wadansu ayyukan da aka gada tun shekaru da yawa tun a zamanin tsohon Gwamna Balarabe Musa da aka jima da yin watsi da su kamar na samawa jama’a Ruwa mai tsafta da za su Sha kuma ayi Ibada da ruwan da a halin yanzu sakamakon babbago da ayyukan nan an cimma nasarar kokarin kammalawa kusan kashi Tamanin zuwa Casa’in na kammalawa don haka ya dace mu kara ba Gwamna hadin kai da goyon baya domin kwalliya ta biya kudin Sabulu kowa ya amfana.
“Muna sa ran idan Allah ya kai mu ga wannan wurin wato a majalisar dokokin Jihar Kaduna za mu kara goya masa baya dari bisa dari muga cewa wadannan ayyukan an ci gaba da su ta yadda mutanen Jihar Kaduna su amfana da ayyukan”.
A game da batun da yake yi na cewa kamar za a yi dauki dora a cikin jam’iyyar APC ace an ba wane takara kuwa, sai Tahir Gambo ya kada baki ya ce shi a fahimtarsa zai yi magana ne da batutuwan da suka fito na zahiri,ko a satin da ya gabata sai da jam’iyya ta jihar Kaduna ta rubuta takarda inda ta bayyana a fili cewa a jihar Kaduna dai wannan maganar babu ita sai dai kawai wadansu mutane kawai da suke ta yawo suna yayatawa, saboda haka mun san mai girma Gwamna adali ne, mun san koda yaushe bayaninsa a kullum shi ne jama’a su zabi wanda suke so mutum mai jama’a wanda zai je ya yi masu adalci domin akwai aiki a gaba ba wai kawai a cikin APC na ne ba ai da akwai zaben duk gari baki daya tare da sauran jam’iyyu da za a yi, to, shi yasa mai girma Gwamna tun da yake bukatarsa ayi wa kowa adalci idan ana zo zaben duk gari baki daya ba na cikin jam’iyyar ba shi yasa muke ta kokarin nemo jama’a domin cikin hukunci Allah kowa ya gane masu irin wadannan maganganun jam’iyya ta rigaya ta fadi kowa ya ji abin da ta ce babu wannan zance babu wannan magana.

“Abu biyu ne wanda dokar zaben ta fadi idan jam’iyyu na son fitar da dan takarar su ko dai su yi zaben Kato bayan kato ko kuma a samu dai daitawa a tsakanin yan takara a cikin jam’iyyar a barwa wanda aka cimma yarjejeniya, kuma duk idan za a dai daita ne a tsakanin yan takara za a nemi kowane dan takara ne a zauna don haka kamar yadda nake gaya wa jama’a da kowa ya sani mai girma Gwamna adali ne duk ya fitar da hikimar da kowa zai ji dadin hakan, don haka abin bukata a samu hadin kai a tsakanin yan jam’iyya, saboda haka a nan abin da nake kokarin fadi shi ne maganar dauki dora babu wannan maganar Sam a cikin jam’iyyar APC don haka kowa zai je ya nemi jama’a ya yi nasa kokarin don jama’a su amshe shi Allah ya bamu Sa’a ya kuma tabbatar mana da alkairi a koda yaushe”, Inji honarabul Tahir.
THESHIELD Garkuwa