Daga Wakilinmu Gamzaki
Gwamnnan Jihar Sakkwato ya mayar da hankalinsa wajen bunkasa harkokin Ilimi ta wajen kashe biliyoyin naira domin gina makarantu da kuma yi wa wadansu ingantattun gyare gyare a fadin Jihar baki daya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, lokacin da yake zagayawa domin duban yadda aikin gina wadansu sababbin ajujuwa da kuma yin ingantaccen gyara ke gudana a makarantar sakandare Jrka ka dawo da ke garin Tambuwal.
Ya bayyana cewa makarantu a duk fadin jihar ana fadadasu da kuma yi wa wadansu gyare gyare na kwarai, ana kuma sake gina wadansu sababbi domin samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.
Bayanin haka na kunshe a cikin wata takardar da mai magana da yawun Gwamnan Sakkwato Muhammadu Bello ya sanyawa hannu.
Tambuwal ya ci gaba da cewa Gwamnatin jihar za ta kara himmatuwa wajen ganin harkar ilimi ta kara bunkasa, ta yadda yara za su samu kyakkyawar makoma a nan gaba domin suma su shiga cikin al’umma mai takama da ingantaccen ilimi.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jama’ar Jihar da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnati da kuma muhimman tsare tsarenta ta yadda za ta kara kaimin samar da ingantattun tsare tsare a dukkan fanni.
Gwamna Tambuwal ya kuma bayyana farin cikinsa da irin yadda ya ga aikin ta fuskar inganci da yadda aikin ke tafiya.
Aikin ya hada da karin ajujuwa, samar da Dakin Gwaje gwaje,babban dakin rubuta jarabawa, Ofisoshin Malamai, Dakin karatu da dai sauransu.
Gwamnan Gwamnan samu rakiyar mataimakinsa Manir Muhammad Dan Iya da sauran manyan ma’aikatan Gwamnati