Home / Labarai / An Nada Sabon Hakimin Faskari A Jihar Katsina

An Nada Sabon Hakimin Faskari A Jihar Katsina

Mustapha Imrana Abdullahi
Maimartaba Sarkin Katsina Alhaji Dr AbdulMumin Kabir Usman ya amince da nadin Malam Aminu Tukur Usman Sa’idu a matsayin sabon Sarkin Yamman Katsina Hakimin Faskari.
Malam Aminu dai ya gaji Mahaifin shi ne, Alhaji Muhammadu Tukur Usman Sa’idu  wanda Allah Ya yi ma rasuwa ranar Juma’a 24 ga watan Janairu 2020.
Muna kuma kara godiya ga Mai martaba Sarkin Katsina bisa wannan karamci da ya yi wa marigayin na ci gaba da raya mashi gida ta mika wannan Sarauta ga dan shi.
Katsina
Wannan ce Takardar da aka amince da nadin sabon hakimin Faskari
Godiya ta musamman ga Baban mu maganin kukan mu, Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari Dallatun Katsina, wanda da amincewar shi ne hakan ta tabbata.
Muna kuma kara godiya ga duk wadanda suka taimaka har hakan ta tabbata.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.