Home / Uncategorized / Gwamna Uba Sani Ya Sake Bude Kasuwar Kidandan A Karamar Hukumar Giwa

Gwamna Uba Sani Ya Sake Bude Kasuwar Kidandan A Karamar Hukumar Giwa

…Ya Shawarci Yan bindiga Su Ajiye Makamai Domin Tsaro 
Daga Imrana Abdullahi
Gwamna Uba Sani ua bayyana jindadinsa sakamakon sake bude kasuwar garin Kidandan da ke karamar hukumar Giwa da ta kasance a kulle tsawon shekaru saboda matsalar tsaro. Gwamnan Wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, Alhaji Sani Liman Kila.
Da yake gabatar da jawabi, Gwamna Sani ya ce wannan kokarin sake bude kasuwar Kidandan a ranar Asabar, ” wata alamace ta Dawowar zaman lafiyaba karamar hukumar Giwa”, ya kuma yi magana a game da sake bude kasuwar Dabnobi ta Birnin Gwari a ranar 29 ga watan Nuwamba, bayan a can baya an kulle ta a tsawon kusan shekaru Goma, hakan ya bayar da damar farfadowar harkokin kasuwanci a yankin baki daya.
Gwamna Sani ya ce hakika zaman lafiya abu ne mai matukar muhimmanci kwarai da ke zaman wata dukiyar da babu kamarta,  domin wani matuidi ne da ke kaiwa ga samun ci gaba iri daban daban a tsakanin jama’ar kasa. Sabanin tashin hankali da ke haifar da dimbin matsaloli masu taron yawa a cikin al’umma, amma kuma zaman lafiya na samar da ci gaba a koda yaushe. Ina farin ciki kwarai bayan samun gagarumin ci gaba a Birnin Gwari sai ga karamar hukumar Giwa ita ma ta biyo baya, hakika zaman lafiya ne mafita”.
Gwamnan ya tabbatarwa da jama’a cewa bangaren wadanda aka tattauna da su na ci gaba da aiki domin tabbatar da samun cimma dukkan abubuwan da aka yi yarjejeniya a kai.
Za a ci gaba da samun dauwamammen zaman lafiya domin amfanin jama’a. Kuma ya ce jami’an tsaro ma na bayar da hadin kai da goyon baya saboda haka duk wanda ya ajiye mukaminsa za a kare shi a kuma yi masa bitar gyaran hali.
Gwaman Sani ya ce sake bude kasuwar Kidandan zai kara taimakawa tattalin arziki ya kuma ba karamar hukumar Giwa wata damar da yawa. Sai ya shawarci jama’a da su rungumi batun hadin kai da taimakon Juna, “Mu duk abu daya ne, duk da za mu iya samu bam-bance bam zancen ra’ayi don haka akwai hanyoyin da za a bi na warware duk wata sarkakiya ko batutuwan da ke bukatar hakan. Don haka ya da ce mu duk mu ce mun ki game da duk wani abu na rashin tashina da zai tayar da hankali don haka ya dace mu hada kai da nufin samar da hanyar ci gaban karamar hukumar Giwa”.
Dokta James Atung Kanyip, kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Kaduna bayani ya yi game da samun zaman lafiya muhimmancinsa a wurin al’umma don haka ya dace kowa ya bayar da gudunmawarsa a samu zaman lafiya.
Shaikh Yuusf Musa Asadussunah, shugaban kwamitin tabbatar da zaman lafiya cewa ya yi bayan an samu yin tattaunawa da dama sosai tare da tarurruka, sai aka samu wannan ci gaban tare da amincewa kuma manyan yan bindiga da mabiyansu duk sun rungumi zaman lafiya. Ya kuma shawarci gwamnati da cewa wadanda suka kasance a tsare amma kuma ba su da laifin komai da jami’an tsaro su sake su.
Da yake gabatar da nasa jawabin shugaban karamar hukumar Giwa, Honarabul Sani Yakawada, godiya ya yi ga Gwamnatin jihar Kaduna da sauran dukkan hukumomin jami’an tsaro, Malaman addinai da sarakunan gargajiya game da irin rawar da duka taka har aka cimma nasarar da aka samu.

About andiya

Check Also

Senator (Barr) Sunday Marshall Katung decries Abduction Of 22 Women And Children

As a result result of too much security challenges in some local Governments in Kaduna …

Leave a Reply

Your email address will not be published.