Home / Big News / Wadansu Mata Sun Hada Kudi Suka Sayi Motar Kai Mata Asibiti

Wadansu Mata Sun Hada Kudi Suka Sayi Motar Kai Mata Asibiti

Wadansu Mata Sun Hada Kudi Suka Sayi Motar Kai Mata Asibiti

Imrana Abdullahi
Wadansu mata da ake kira mata masu hankali, ilimi tare da dimbin basira sun yi Kudi Kudi domin sayen motar daukar matan da ke dauke da ciki lokacin haihuwa
Su dai matan daga Jihar Jigawa sun hada kai ne inda suke amfani da motar da suka saya a kan kudi naira miliya daya domin kai mata asibiti musamman a lokacin haihuwa
Matan da Duke zaune a kauyen Bordo cikinnkaramar hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Su dai matan sun hada kudi ne a kalla naira dubu 1000 a tsakaninsu suka sayi motar naira miliyan 1.

Majiyarmu ta shaida mana cewa matan sun hada kansu ne inda suka yi tunanin samun mota domin samun motar daukar mata zuwa asibiti a lokacin nakuda idan za su haihuwa.

Bayanan da muke samu dai sun tabbatar mana cewa matan na samun wahala ne wajen kai mata asibiti lokacin haihuwa da asibitin ke da tsawon kilomita 29 daga kauyensu.

Kamar yadda majiyarmu ta bayyana mana cewa matan na zuwa asibitin ne idan ta hanyar yin amfani da Keke kamar yadda majiyar ta shaida mana.

About andiya

Check Also

APC SOKOTO FLAGS OFF STATE-WIDE CAMPAIGN IN WAMAKKO LG, UNVEILS 8-POINT AGENDA

  The All Progressives Congress (APC), Sokoto State chapter on Wednesday flagged off its state-wide …

Leave a Reply

Your email address will not be published.