Home / Big News / Gwamnan Bauchi Na Dauke Da Cutar Korona Bairus

Gwamnan Bauchi Na Dauke Da Cutar Korona Bairus

Imrana Abdullahi

Ya zuwa yanzu dai bayanan da ke fitowa daga fadar Gwamnatin Jihar Bauchi da ke arewacin tarayyar Nijeriya na cewa Sanata Bala Abdulkadir Mohammed na dauke da cutar Korona bairus.

Kamar dai yadda babban mai taimakawa Gwamnan a kan harkokin yada labarai, Muktar Gidado ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata cewa hakika Gwamnan ya harbu da cutar.

Wannan itace takardar da Muktar Gidado ya fitar da ke sanarwa Gwamnan Bauchi lallai ya harbu da cutar

Kafin a kammala yi wa Gwamnan Gwaji dai an ji shi da kansa yana cewa ya hadu da Mohammed da ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da aka yi wa Gwaji aka kuma tabbatar ya harbu da cutar shima a ranar Lahadin da ta gabata.

About andiya

Check Also

Sultan urges muslims, Nigerians to reconcile selves for peace, unity says ‘don’t allow politics  divide you’

By Suleiman Adamu, Sokoto Ahead of the Ramadan fast around the corner, the Sultan of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.