Home / Lafiya / Ana Saran Yi Wa Gwamnonin Katsina Da Kogi Gwajin Korona Bairus

Ana Saran Yi Wa Gwamnonin Katsina Da Kogi Gwajin Korona Bairus

Mustapha Imrana
Kamar yadda wadansu kafafen yada labarai na tarayyar Nijeriya ke ta wallafa bayanai cewa akwai bukatar a Killace tare da yi wa wadansu Gwamnoni da wasu muhimman mutane Gwajin cutar Korona birus.

Hakika a wannan hoton ya tabbatar da gaskiyar maganar da ke nuni da bukatar a yi Gwajin domin tantance irin matsayin lafiyarsu game da cutar Convid 19 da ake kira Korona Bairus.
Saboda kamar yadda Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ya tabbatar wa da duniya killace kansa sakamakon gaisawar da ya yi da Muhammad Atiku Abubakar a Legas kuma suka shigo Jirgin sama zuwa Abuja amma bayan an Gwada Gwamnan Bauchi an same shi da harbuwa da wannan cuta ta Covid 19.
Kamar dai yadda wata kafar yada labarai ta bayyana cewa wasu mutane da suka hada da Gwamnonin katsina da Kogi sun gana da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Nijeriya Abba Kyari da shima aka same shi da harbuwa da cutar tun bayan da ya dawo daga ketare inda ake kyautata zaton a can ya dauko cutar Covid 19.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.