Related Articles
Daga Imrana Abdullahi Kaduna
Bayanan da ke fitowa daga gidan Gwamnatin Jihar Kaduna kuma daga bakin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I ya tabbatarwa duniya cewa ya harbu da cutar Covid 19 da ake kira Korona Bairus
Gwamnan Kaduna ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar da kansa mai dauke da sa hannunsa kuma gashi a cikin bidiyo yana tabbatarwa duniya cewa sakamakon kwajin da aka yi masa na Cutar Korona Bairus ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Korona bairus.
A cikin sanarwar Malam Nasiru ya bayyana cewa duk da ba zato ba tsammanin cewa yana dauke da cutar amma sai gashi ya harbu da cutar.
Gwamnan a cikin faifan bidiyon da ya bayyana ya sanar cewa mataimakiyarsa za ta ci gaba da aikin kwamitin da aka nada domin yaki da wannan Covid – 19 Korona Bairus.