Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari zai halarci taron bitar da aka shiryawa Limaman masallatan Juma’a.
Kamar yadda wata takardar sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Alhaji Abdu Labaran Malumfashi ya sanyawa hannu cewa za a yi taron bitar ne a gobe Talata 25, ha watan Fabrairu, 2020 a babban dakin taro na hukumar kula da kananan hukumomi da misalin karfe sha daya na safiya idan Allah ya kaimu.
Sanarwa Alhaji Abdu Labaran Malumfashi Darakta Janar mai kula da harkokin kafafen yada labarai na Gwamnan Jihar Katsina.