Home / Labarai / GWAMNAN ZAMFARA YA CE A RIKA KIRANSA DAUDA LAWAL

GWAMNAN ZAMFARA YA CE A RIKA KIRANSA DAUDA LAWAL

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Kamar dai irin yadda babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara a kan harkokin yada labarai Mustapha Jafaru Kaura ya fitar da wata sanarwa da aka mikawa kafafen yada labarai cewa
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai da yada labarai Mustapha Jafaru Kaura ya sanyawa hannu kuma ya mika wa domin sanar da kafofin yada labarai da suke aiki a ciki da wajen Jihar Zamafar su Sani cewa daga yanzu za a rika kiran Gwamnan Jihar Zamfara a matsayin Dauda Lawal Kawai.

Kamar yadda sanarwar ta tabbatar “Wannan shine don sanar da jama’a musamman Kungiyoyin Watsa Labarai da ke aiki a ciki da wajen Jihar cewa daga yanzu za a kira Gwamnan Jihar Zamfara a matsayin Dauda lawal kawai”. Inji sanarwar.

“Duk sauran ka’idojin da aka danganta da sunansa kafin mukaminsa na Gwamnan jihar ya kamata a daina wanzuwa , wannan umarni ya kamata ya shafi duk kafofin yada labarai na ciki har da sabbin kafofin watsa labarai na zamani da suke a yanar Gizo da kuma kafofin Sada zumunta na sadarwa”, inji sanarwar da Mustapha Jafaru Kaura ya sanyawa hannu kuma ya fitar.

About andiya

Check Also

GWAMNA DAUDA LAWAL YA HARAMTA HAƘAR MA’DINAI BA BISA ƘA’IDA BA

…YA UMURCI JAMI’AN TSARO SU ƊAUKI TSATTSAURAN MATAKI Daga Imrana Abdullahi A yau Asabar, Gwamnan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.