Home / Labarai / BAN BAYYANA KADARORIN TIRILIYAN 9 BA – GWAMNA ZAMFARA

BAN BAYYANA KADARORIN TIRILIYAN 9 BA – GWAMNA ZAMFARA

Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon irin yadda wadansu mutane da suka shahara wajen yada jita – jitar cewa wai Dokta Dauda Lawal Dare, Gwamnan Jihar Zamfara ya bayyana cewa tsakanin makudan kudi kasa da kuma Kaddarori ya na da naira biliyan tara.

Gwamna Dauda Lawal Dare ya fito fili ya bayyana cewa hakan ba gaskiya ba ne babu wani abu mai kama da hakan da za a ce shi ne ya fade shi a ko’ina.

 An  ruwaito cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal-Dare, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa ya bayyana kadarorin da ya kai Naira tiriliyan Tara.

Kamar dai irin yadda ake ta yada wa cewa wasu na ta yada cewa wai Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya bayyanawa a hukumace cewa ya na da dukiyar da ta kai naira tiriliyan Tara, wanda ya tabbatar da hakan ba gaskiya ba ne.

A bisa wannan dalilin ne yasa mai magana da yawun Dauda Lawal-Dare, a cikin wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai, Sulaiman Bala Idris, a ranar Juma’a, ya bayyana labarin a matsayin kage na karya da aka shirya domin kawar da hankalin sabuwar Gwamnati daga tafarkin ceto Zamfara.

Sanarwar  ta ce ci gaba ne da karyar da wadanda suka fadi zabe suka yi, kamar yadda suka yi a lokacin yakin neman zabe.

Mai magana da yawun Gwamnan ya kara da cewa sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali wajen ganin ta kawo hazakar da ake bukata a harkokin mulki a jihar domin gudanar da aikin da aka dora mata.

“An ja hankalinmu kan wani mugun labari da aka dasa aka watsa a kafafen sada zumunta na zamani cewa Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana kadarorin da ya kai Naira Tiriliyan Tara.  Gwamnati ta takura ta fitar da wannan sanarwa domin ance karyar da ake ta maimaitawa (kuma ba a kalubalanci) ta kan kai ga gaskiya.

“Wannan karyar karya ce da aka kirkira kuma aka tura ta a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne ta hanyar bata gari da ke da niyyar karkatar da sabuwar gwamnati.

“Sharuɗɗan da suka shafi bayyana kadarorin suna cikin ka’idojin da’a na jami’an gwamnati, wanda ke kunshe a cikin sashe na 1 na Jadawali na Biyar na Kundin Tsarin Mulki na shekarar 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima dole ne ya dace da duk ma’aikatan gwamnati kuma yana nan a tsare a tsaren hukumar kula da Da’ar ma’aikata.

“Dukkan jami’an gwamnati tun daga Shugaban kasa, Mataimakin Shugaban Gwamnoni duk zababbun jami’ai da ma’aikatan gwamnati dole ne su cika su gabatar da fom din bayyana kadarorin kamar yadda doka ta tanada.  Dauda Lawal ya bi ka’idojin kundin tsarin mulki kuma abubuwan da ke cikin su na kasancewa amintacciya ga ofishin, wata hukuma mai mutuntawa da kwarewa.

“Ba za a yi amfani da irin wadannan labaran karya na kafafen sada zumunta ba, domin gwamnatinmu ta kuduri aniyar kuma ta mai da hankali kan kudirinta na magance matsalar tsaro, ilimi, ruwan sha, kiwon lafiya, noma da sauran kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da suka addabi jihar.  Muna kuma aiki ba dare ba rana domin ganin mun sauke nauyi da ayyukan da Gwamna ya rantse da su.

“Muna kan aikin kuma muna da ginshiki da yawa da za mu yi a kokarinmu na ceto da sake gina jihar Zamfara mai inganci da kuma ci gaba da mai da hankali wajen ganin mun cika aikinmu.  Muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan karyar da ake yadawa da gangan domin a karkata da bata sunan wannan sabuwar gwamnati a jihar Zamfara,” inji sanarwar.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.