Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya nuna alhinin sa bisa ibti’in gobarar da ta yi sanadiyyar rasuwar wasu almajirai 17 a jihar.
A ƙalla wasu almajirai 17 ne suka rasa rayukan su a wata makarantan allo da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda sakamakon wata mummunar gobara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu Larabar nan, ya bayyana cewa Gwamnan ya nuna wannan ibtila’i a matsayin abin takaici.
Sanarwar ta ambota Gwamna Lawal yana cewa, “Na kaɗu matuƙa da jin gobarar da ta tashi a makarantar Malam Ghali, wata makarantar almajirai da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.
“A madadin gwamnatin jihar Zamfara, ina miƙa ta’aziyyar mu ga iyalai, makaranta da ma dukkan ƙasar nan baki ɗaya bisa wannan rashi na waɗannan yara.
“Ina addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya ƙara wa iyaye da ‘yan uwan waɗannan yara haƙurin jure wannan rashi. Ina kuma addu’ar Allah ba waɗanda ke kwance a asisibi lafiya.
“A matsayin gwamnatin mu mai sanin ya-kamata, za mu yi nazari domin gano musabbabin wannan gobara don a ɗauki matakan kare aukuwar lamarin nan gaba.
“Za mu bayar da duk gudumawar da ta wajaba ga iyalan waɗanda abin ya shafa.”