Home / Labarai / “Gwamnan Zamfara Ya Yi Gaggawar Ajiye aikinsa Ko Ya Fuskanci Kotun Duniya”

“Gwamnan Zamfara Ya Yi Gaggawar Ajiye aikinsa Ko Ya Fuskanci Kotun Duniya”

….Muna Son  A Sanya Dokat Ta Baci A Jihar Zamfara
Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu da ke fafutukar kare hakkin jama’a, karkashin jagorancin African Youth For Conflict Resolution And Prevention sun yi kira ga Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ta hanzarta daukar matakin ceton dimbin jama’ar Jihar Zamfara ta hanyar Sanya dokar ta baci a Jihar Zamfara.
Gamayyar kungiyoyin karkashin jagorancin African Youth For Conflict Resolution and Prevention ta bakin Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, sun bayyana cewa yin wannan kiran ya zama wajibi domin Gwamnatin tarayya ta hanzarta daukar matakin ceto al’ummar Jihar Zamfara daga halin da suke ciki na tabarbarewar matsalar tsaron lafiya da dukiyarsu a jihar.
“Saboda ta yaya a lokacin da matsalar tsaro ke samun al’ummar Jihar Zamfara lamarin da ya zame masu larura amma sai ga Gwamna Dauda Lawal ya ta fi wajen bikin inda ake ta wake wake ana yin watsi da kudi wanda hakan ba abin da ya dace ba ne. Da Dauda zai ga ne ai da irin wadannan kudin an je an taimakawa jama’a da su ne wajen sama masu abinci da abubuwan bukatun larurar yau da kullum da lamarin ya fi ma’ana”.
Dokta Shinkafi ya ci gaba da bayanin cewa a can baya lokacin da Matawalle ya na shugabanci a Jihar akwai lokacin da aka yi watanni akalla Tara ba a samu wata matsalar rasa rayukan jama’a ba, wanda a fili take kowa ya shaida hakan.
“Sabanin irin abin da ke faruwa a halin yanzu da jama’ar Jihar suka shiga cikin wani mawuyacin hali na kashe kashe da satar jama’a tare da dukiyarsu amma wanda ke da hakkin ba su kariya ya kasa daukar matakin da ya dace a dauka ssi tafiye tafiye kawai duk da jama’ar da yake yi wa jagoranci na cikin akuba”.
“Muna nan muna hada bayanan da zamu wuce domin kai kara kotun duniya. Muna da yawan alkalumman wadanda suka rasa rayukansu da kuma duk irin matsalolin tsaron lafiya da dukiyar jama’ar Jihar.
Dokta Shinkafi ya shaidawa manema labarai cewa ko shakka babu za su kai kara kotun duniya ta ICC da kuma ECOWAS da nufin kwato hakkin mutanen Jihar Zamfara Maza da Mata, Yara da manya.
Kuma akwai wani hanzari ba gudu ba ta yadda “Gwamna Dauda Lawal ya ce shi ba zai yi sulhu da yan Ta’adda ba. Amma sai ga shi ya na aika wadansu mukarraban Gwannatinsa a sirri suna yin tattaunawa da wadanda ya fito fili ya na cewa ba zai yi sulhu da su ba duk mun samu sahihan bayanan irin abubuwan da ke faruwa.
“Ko a lokacin da aka yi Yakin duniya na farko da na biyu ai duk ssi da aka zauna aka yi Sulhu sannan aka samu warwarewar matsalar Yakin don haka, muke ganin Dauda bai samu da rayuwar jama’a  bane shi ya sa bai daukar wani mataki a game da halin da suke ciki ba, koda yake kotun duniya da ECOWAS na nan kuma zamu je”.
“Muna kuma kara jaddada yin kira ga shugaba Bola Ahmad Tinubu da ya Sanya dokar ta baci a Jihar Zanfara a kawo kantoman mulkin  soja ya rike Jihar Zamfara a tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar jama’a a kowane mataki na Jihar”. 

About andiya

Check Also

Relentless attempt to ridicule Ganduje futile, must stop — Group

  By; Our reporter A group under the auspice of Kano Concerned Forum has faulted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.