Home / Kasuwanci / Gwamnatin Jigawa Ta Yafewa Kananan Masana’antu Haraji

Gwamnatin Jigawa Ta Yafewa Kananan Masana’antu Haraji

Imrana Abdullahi
Kwamishinan kudi na Jihar Jigawa Babangida Umar Gantsa ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ta yafewa daukacin kanana da matsakaitan masana’antu Jihar kudin haraji na tsawon shekara daya.

Kamar dai yadda Kwamishinan ya bayyana cewa an yi wannan tsari ne domin samar wa kanana da matsakaitan masana’antu su samu saukin gudanar da harkokinsu, bisa la’akari da irin ci gaban da suke kawo wa a rayuwar al’umma baki daya.

Kwamishina Umar Gantsa sai dai ya ce yafiyar harajin bata shafi na kungiyoyi masu zaman kansu ba

About andiya

Check Also

CCMMD Urges Unified Action to End Gender-Based Violence in Nigeria Amidst UN 16 Days of Activism with Hope and Action

As the world commence the celebration of International Day for the Elimination of Violence against …

Leave a Reply

Your email address will not be published.