Home / News / GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA KADDAMAR DA SAYAR DA TAKIN ZAMANI A FARASHI MAI SAUKi 

GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA KADDAMAR DA SAYAR DA TAKIN ZAMANI A FARASHI MAI SAUKi 

 

Noma Tushen Arziki, Kamar Yanda Hausawa Ke Fad’i.

 

 

Hakam Ne Ma Ya Sa Gwamnatin Jihar Bauchi Karkashin Jagorancin Senator Bala Muhammed CON (Kauran Bauchi Jagaban Katagum) Ba Ta Yi Kasa A Gwiwa Wajen Ganin Ta Inganta Wannan Fanni Ba.

 

 

Saboda Bayar Da Muhimmanci A Bangaren Noma, Cikin Ikon Allah Da Ranar Yau Alhamis Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kaddamar Da Siyar Da Takin Zamani Wa Manoma Domin Tunkarar Daminar Bana.

 

 

Lokacin Da Ya Ke Kaddamar Da Siyar Da Takin A Cikin Garin Soro Da Ke Karamar Hukumar Ganjuwa, Gwamnan Al’ummar Jihar Bauchi, Senator Bala Muhammed, CON (Kauran Bauchi Jagaban Katagum), Ya Tabbatar Da Cewa GwamnatinSa Za Ta Samar Da Wadataccen Takin Zamani, Sannan Za Ta Sayarwa Manoman Jihar A Farashi Mai Rahusa. Kana, Gwamnan Ya Kara Jaddada Aniyar Gwamnatin Jihar Na Cigaba Da Bunkasa Harkar Noma A Fad’in Jihar Bauchi.

 

 

Wannan Kaddamarwan Ya Biyo Bayan Saka Zunzurutun Kudi Mai Yawa Da Gwamnatin Jihar Ta Yi Domin Samar Da Takin Zamanin Wa Manoman, Domin Su Samu Damar Gudanar Da Harkokin Noman Su Cikin Walwala Da Kuma Kwanciyar Hankali.

 

 

Saboda Karfafawa Manoman Jihar Gwiwa, Gwamnatin Jihar Za Ta Dinga Sayarwa Da Takin Zamanin Cikin Farashi Mai Rahusa, Inda Za Ta Sayar Da NPK A Kan Farashin Naira Dubu Tara (9,000), Yayin Da Notore Urea Gwamnatin Za Ta Sayar Da Shi A Kan Farashin Naira Dubu Goma Sha D’aya (11, 000).

 

 

Wani Abin Birgewan Kuma Shine; Kauran Bauchi Ya Ce Gwamnatin Jihar Za Ta Dinga Ware Kaso Goma Cikin Kasafin Kudin Jihar Domin Samar Wa Manoma Ingantaccen Iri.

 

 

Wannan Taro Mai Matukar Muhimmanci Ya Samu Halartar Mai Girma Mukaddashin Gwamna Sanata Baba Tela (Wakilin Ayyukan Bauchi Matawallen Katagum), Sarakunan Gargajiya, Sakataren Gwamnatin Jiha Ibrahim Muhammad Kashim, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati Dr. Aminu Hassan Gamawa, ‘Yan Majalisun Dokoki, Manyan Jami’an Gwamnati, Shuwagabannin Al’umma Maza Da Mata, Masu Bawa Gwamna Shawara, Mataimaka Na Musamman Da Kuma Dubban Masoya Da Magoya Baya.

 

 

Muna Addu’ar Allah Shi Cigaba Da Taimakon Wannan Gwamnati Wacce Ba Ta Yi Kasa A Gwiwa Wajen Ganin Ta Gina Sabuwar Jihar Bauchi Ba.

Jamilu Barau Daga Bauchi

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.