Home / News / Biyayya Ga Abdul’Aziz Yari Wajibi Ne – Dokta Suleiman Shinkafi

Biyayya Ga Abdul’Aziz Yari Wajibi Ne – Dokta Suleiman Shinkafi

….Ba Mu San Kowa Ba Sai Abdul’azizi Yari

Mustapha Imrana Abdullahi
“Ba mu san kowa ba sai Abdul’Aziz Yari, Alhaji Mamuda Aliyu Sh9nkafi,Sanata Kabiru Mafara, Dauda Lawal Dare,Sagir Hamidu da kuma Ibrahim Shehu Bakauye su ne masu dimbin jama’a duk fadin Jihar Zamfara, don haka idanun shugabannin APC na kasa baki daya su bude”.
An yi kira ga daukacin shugabannin jam’iyyar APC na Kasa karkashin jagorancin Gwamnan Yobe Mai Mala Buni da kada su bari a samu matsalar shugabancin jam’iyya a Jihar Zamfara.
Saboda kamar yadda kowa ya Sani babu wanda bai san nagoya bayan da Abdul’aziz Yari, Alhaji Mamuda Aliyu,Sanata Kabiru Marafa,Dauda Lawal Dare da Honarabul Shehu Bakauye (Phd) su ne masu magoya baya a duk fadin Jihar Zamfara.
Ba dai- dai ba ne Gwamna Mai Mala Buni ya yi saurin yanke hukuncin cewa Gwamna Muhammad Bello Muhammad Matawalle ne shugaba ko kuma jagora.
A Dama Alhaji Abdul’Aziz Yari tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kenan tare da Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi
” Shin idan aka yi wa Mai Mala Buni tambaya wa ya Sani a Jihar Zamfara? ai bai san kowa ba
Sako na ga Mai Mala Buni kada ya yi mana shisshigi a Jihar Zamfara, domin Jihar Zamfara ba Yobe bace, saboda mun san halin da Jiharsa take ciki domin na zagaya Jihar Zamfara.
Ya dace duniya ta Sani cewa magoya bayan su Abdul’Aziz Yari, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi,Dauda Lawan Dare, Honarabul Ibrahim Shehu Bakauye duk su ne magoya bayan Buhari.
Yadda kasan Sallah na wajibi gare mu haka biyayya ga Abdul’azizi Yari ta zama wajibi gare mu domin kowa ya san hakan.
Kuma duk wadanda Buhari ya ba mukamai a siyasa kamar ministoci da sauran mukaman Gwamnatin tarayya babu wanda yake da jama’a kamar Abdul’aziz Yari sabida shi ya rike jama’a kuma shi kowa ke yi saboda nagartarsa.
“Ko za mu rasa rayukan mu sai mun ci gaba da biyayya ga Abdul’Aziz Yari ko za a rasa rai sai mun yi wa Abdul’aziz Yari Biyayya kamar  ba Gobe”.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.