Home / News / Yari, El-Rufa’ Da Marafa Sun Kalubalanci Kalamin Shugaban Rikon APC Mai Mala Buni

Yari, El-Rufa’ Da Marafa Sun Kalubalanci Kalamin Shugaban Rikon APC Mai Mala Buni

Mustapha Imrana Abdullahi
Sanata Kabiru Marafa jigon jam’iyyar APC daga Jihar Zamfara ya bayyana cewa dukkansu wato mutane uku da suka yi tattaunawar hadin Gwiwa da kafar yada labarai ta bbc sun kalubalanci Kalamin da shugaban rikon APC na kasa ya yi a Jihar Zamfara cewa Gwamna Matawalle ne jagoran APC a Jihar.
Sanata Kabiru Marafa ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da gidan Talbijin na “Arise” game da dambarwar siyasar da ke faruwa a Jihar Zamfara a halin yanzu sakamakon Cewar da Gwamna Muhammadu Bello Matawalle ya yi na komawa jam’iyyar APC daga PDP.
Sanata Kabiru Marafa ya ce tun farko sun yi matsaya inda suka ce ba za su halarci taron karbar Gwamna Muhammadu Bello Matawalle ba a ranar Talatar da ta gabata, amma saboda irin yadda wadansu Gwamnoni guda shida da kuma wasu tsofaffin Gwamnoni guda uku suka taru a gidan tsohon Gwamna Abdul’Aziz Yari, sannan shi kuma Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ya kira shi inda ya shaida masa cewa an umarce shi ne daga fadar shugaba Buhari ya yi magana da shi, ya sa suka amince Yari ya je Zamfara amma ba maganar da Mai Mala Buni ya yi.
Sai kuma “lokacin da su shugaban rikon APC Mai Mala Buni yake kan hanyarsa ta zuwa Zamfara domin karbar Gwamna Matawallen Maradun a matsayin wanda zai shiga APC duk sun yi magana a waya da shi da Mai Mala Buni cewa babu batun ace Gwamna Matawalle na Zamfara shi ne shugaban tafiya, amma abin mamaki sai ga Gwamna Mai Mala Buni ya aikata abin da ya sabawa yarjejeniyar tun farko don haka ba za ta sabu ba, a cikinsu ba wanda zai amince da wannan kalami na Mai Mala Buni”.
Ko shi “Mai Mala Buni, ya dace ya Sani cewa akwai kalubale a game da zamansa shugaban rikon APC na kasa domin tsarin mulkin jam’iyya ya yi masa togaciya da zama shugaba, kuma na yi wa shugaba Buhari wannan maganar domin za ta iya tasowa”.
“Tun da farko sai da muka ce idan Abdul’Aziz Yari ya amince ya je wajen wannan taron ya ta fi ne da yawun kansa kawai shi kadai, domin mun tara mutane sama da dari shida a Kaduna an yi taron tuntuba domin mu ji ina ne ra’ayin yayan jam’iyya da suka kasance su ne masu ita, me suke bukatar ayi kuma an yi an cimma matsaya to kuma ta yaya kawai da rana tsakiya za a rika canza mana matsayar da masu jam’iyya suka cimma?
Kabiru Marafa ya ci gaba da cewa ya dace fa kowa ya daina mancewa da PDP fa bata ta ba cin zabe a Jihar Zamfara ba, saboda haka ake kokarin a koma jam’iyyar da muka yi wahalar kafawa muka yi mata duk abin da yakamata har jama’a suka rungume ta suka amince da ita har ake sha’awar a shiga cikinta”.
Kuma hukuncin kotun kolin Najeriya ta tabbatar da cewa babu jam’iyyar APC a zaben da aka yi a Jihar Zamfara a shekarar 1219 don haka ta yaya wani zai ce shi ne Gwamna kuma a karkashin APC a da duba sosai domin gudun yin kitso da kwarkwata.
Saboda haka muke yin kira ga Mai Mala Buni da ya rika takawa a sannu a hankali kada ya rika tsammanin Jihar Zamfara kamar kowace jiha ce, lallai – lallai lamarin ba haka yake ba domin Jihar zamfara da ban ce a ci gaba da sanin hakan.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.