Home / Labarai / Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Amince Da Dokar Kisa Ga Duk Wanda Ya Yi Wa Yara Fade

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Amince Da Dokar Kisa Ga Duk Wanda Ya Yi Wa Yara Fade

Mustapha Imrana Abdullahi

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kafa dokar yin hukuncin kisa ga duk wanda ya yi wa kananan yara fade.

 

 Karkashin sabuwar dokar da Gwamnatin Jihar ta kafa, wadanda aka Yankewa hukuncin yi wa kananan yara fade da suka kasance kasa da shekaru 10 za a yanke masu hukuncin kisa ne ba tare da wani zabi ba.

 

Kwamishinan shari’a na Jihar kuma babban mai shari’a, Dokta Musa Adamu wanda shi ne ya bayyana wannan hukuncin a wajen wani taron manema labarai a ranar Laraba 29 ga watan Disamba 2021, ya bayyana cewa ma’aikatarsa ta karbi korafi wanda ke rubuce a cikin littafinta na kararraki da suka kai 196 an kuma samu shirya kararraki vida 178 da aka bayar da shawarar shari’a”.

 

 

Adamu ya ce; 

” A farkon wannan shekarar Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya Sanya wa dokar da ta yi hanin hannu dokar dai ta bayyana hukuncin kisa ne ga duk wanda ya yi fade amma da zabin tara.Amma kwanan nan Gwamnatin ta kuma Sanya wa dokar kare kananan yara da ta yi bayanin cewa hukuncin kisa ga duk wanda ya yi wa kananan yara masu kasa da shekaru 10 hukuncin kisa”.

 

“Daga cikin yawan litattafan karar da ake da su gida 90 masu dauke da karar fade; 27 kulfabul homisid ne; sai luwadi 31; satar mutane da ake da guda 18; fashi da makami guda 20 sai batun karya dokar tuki guda 2.

“Ma’aikatar shari’ar ta samu yin kariya ga Shari’u 25 a gaban kotun daukaka kara da ke shiyyar Kano, an kuma yi nasarar kammala shari’ar manyan laifuka 83 da ke gaban babbar  kotu shari’a guda Takwas da ke Birnin Kudu, Dutse,Gumel,Hadejia,Kazaure da Ringim. An Yankewa guda 34 hukunci sai kuma guda 49 da suke yi kariya an sallamesu saga Shari’ar”.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.