Home / Kasuwanci / Gwamnatin Jihar Katsina Ta Dau Mataki A kan Masu Boye Shinkafa

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Dau Mataki A kan Masu Boye Shinkafa

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana damuwarta kan abin da wasu ‘yan kasuwa masu sayar da shinkafa a jihar ke yi, inda suka koma yin babakere.  Wannan ci gaban ya zo ne bayan rufe dukkan iyakokin Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a kasar da ke makwabtaka da Jihar.

A wata sanarwa da Ibrahim Kaula Mohammed, mai magana da yawun gwamna Dikko Umaru Radda ya fitar, an lura da cewa da gangan wasu masu sana’ar shinkafa da dillalan shinkafa ke haifar da karancin ta domin rashin adalci wajen tayar da farashi don cimma burinsu na son kai.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A daidai lokacin da gwamnatin jihar Katsina ta himmatu matuka wajen ganin ta rage radadin tsadar rayuwa da suka hada da raba buhunan hatsi dubu 39,100 ga masu karamin karfi ta hanyar kwamitoci na musamman a matakin Unguwa, abin takaici ne, don ganin wasu mutane suna lalata wannan ƙoƙarin. “

Gwamnatin ta kuma yi karin haske da cewa ba za ta lamunta da irin wadannan abubuwa da ke kawo tabarbarewar zaman lafiya da kuma kawo cikas ga rayuwar al’ummarta ba.  Don magance wannan batu, an kaddamar da wani shiri na sa ido na musamman da ya shafi hukumomin tsaro daban-daban domin gano tare da daukar matakin da ya dace kan wadannan masu zagon kasa ga tattalin arziki da kuma kyawawan shirye shiryen Gwamnati.

An yi kira ga jama’a da su ba da hadin kai tare da baiwa hukumomin da abin ya shafa duk wani ingantaccen bayani da zai taimaka wajen gano irin wadannan masu zagon kasa.

Sabida ta yin haka ne gwamnati za ta iya magance wannan mummunar dabi’a da ta saba wa tsarinta na bayar da agaji da tallafi ga daukacin al’ummar Jihar Katsina baki daya.

“Gwamnati na fatan wadanda suke aikata wannan aika-aika za su sake duba ayyukansu tare da hada hannu da hukumomi wajen samar da ingantaccen yanayin tattalin arziki da walwalar jama’a”, inji takardar da Ibrahim Kaula ya sanyawa hannu.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.