Home / Labarai / Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Tallafawa Yan Kasuwar Da Suka Yi Gobara A Sakkwato Da Miliyan 30

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Tallafawa Yan Kasuwar Da Suka Yi Gobara A Sakkwato Da Miliyan 30

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Tallafawa Yan Kasuwar Da Suka Yi Gobara A Sakkwato Da Miliyan 30

 Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abibakar Atiku Bagudu ya taimakawa yan kasuwar Sakkwato da suka yi Gobara a ranar Talata da Safe ya taimaka da kudi naira miliyan 30.

Gobarar dai ta tashi a babbar kasuwar garin Sakkwato inda ta lashe Dukiya mai yawa.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Muhammad Bello mai bayar da shawara ga Gwamna Tambuwal kan harkokin kafafen yada labarai.

Gwamna Bagudu, ne cikin manyan mutane da ya ziyarci wannan kasuwa domin yi wa yan kasuwa da Gwamnatin Jihar Sakkwato jajen abin da ya faru.

Ya ce ziyarar da ya kawowa Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kawo ta ne domin jajantawa Gwamnati da kuma al’ummar Jihar Salkwato, inda ya kara da cewa dukkan abin da ya shafi Jihar Sakkwato ya shafe shi.

Da yake mayar da jawabi Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Godiya ya yi ga tare da bayyana wannan tallafi da cewa alamace ta kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsu da kuma yan uwantaka da ke tsakanin Jihar Sakkwato da Kebbi.

Ya ci gaba da bayanin cewa a wannan lokacin babu wani rai da aka rasa sakamakon tashin Gobarar, Gwamna Tambiwal ya ce jami’an kashe Gobara da suka hada da na Gwamnatin Jihar Sakkwato da Gwamnatin tarayya da kuma na babban filin Jirgin saman kasa da kasa Sultan Abubakar na uku, duk sun kawo gudunmawa wajen aikin shawo kan Gobarar.

Ya kuma bayyana farin ciki tare da gamsuwa da aikin jami’an tsaro a wajen wannan Gobara musamman ganin irin yadda suka yi tsayuwar daka domin tabbatar da tsaro a wannan kasuwa da Gobara ta tashi.

Gwamna Tambuwal ya roki Allah da ya ci gaba da taimakawa Gwamna Bagudu tare da jama’ar Jiharsa baki daya.

Gwamna Tambuwal ya kuma jagoranci Gwamnan Jihar Kebbi tare da tawagarsa zuwa kasuwar da Gobarar ta tashi, inda Bagudun shi kansa ya jajantawa yan kasuwar da lamarin ya shafa.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.