Home / KUNGIYOYI / Gwamnatin Jihar Zamfara ta jinjiwa Kungiyar kwadago ga me da Asuu

Gwamnatin Jihar Zamfara ta jinjiwa Kungiyar kwadago ga me da Asuu

Daga Hussaini Ibrahim,Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara,Karkashin jagorancin mukaddashin Gwamna Muhammadu Bello Matawallen Maradu da mataimakinsa Sanata Hassan Nasiha ta jinjiwa Kungiyar kwadago NLC reshen Jihar Zamfara, saboda fafutukar ganin an kawo karshen yajin aikin Malam Jami’oin Kasar Najeriya.
Mukaddashin Gwamnan Sanata Hassan Nasiha ya kara da cewa, Kungiyar NLC ta yi abin da ya cancanta wajan ganin rayuwar matasa ta inganta sun samun ingantace ilimi da zai mai dasu mutane na gari,dan samun ingantaciyar rayuwar al’umma a nan gaba.dan ‘ya’yan masu karatun a jami’ar Kasar nan sune fatar mu a nan gaba da zasu raya wannan Kasa tamu.inji Sanata Hassan Nasiha.
“Sanata Hassan Nasiha ya kuma tabbatar wa Kungiyar NLC ta Jihar Zamfara,cewa,wannan tahardar koke da suka bada zai mikata ga mai gidansa Gwamna Matawallen Maradu dan ya isarwa Shugaban Kasa dan kawo karshen yajin aikin Malaman Jami’oin Kasar.
Anasa jawabin , Shugaban Kungiyar NLC reshen Jihar Zamfara,Kwamaret Sani Haliru ya bayyana cewa, gwamnatin Kasar nan batajin a jikinta Sai  an motsata ta hanyar jerin gwano,kungiyoyi da dama da manyan Kasar nan sun sa baki wajan magance matsalar yajin aikin Malaman Jami’oin Amma abun yaci tura,shi yasa Muka Foto ayau dan nuna bakin cikin mu game da yadda ake neman bata rayuwar matasa Kasar na Ko in kula akan matsalar karatun su,dan haka muna shedawa gwamnatin cewa, wannan jerin gwano na gargadi ne akan ta kawo karshen yajin aikin Malaman Jami’oin idan ba haka ba zamu tsaida kasar nan cak.indan kune yaji jiki ya tsira inji Kwamaret Sani Haliru.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.