Home / Labarai / Gwamnonin Arewa Sun Jinjinawa Matasan Arewa 

Gwamnonin Arewa Sun Jinjinawa Matasan Arewa 

Gwamnonin Arewa Sun Jinjinawa Matasan Arewa 
Imrana Abdullahi
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin tarayyar Nijeriya Gwamnan Jihar Filato Mista Simon Bako Lalong, ya bayyana irin farin ciki da jin dadin da Kungiyoyin matasan Arewacin tarayyar Nijeriya suka nuna karkashin jagorancin Nastura Ashiru Sharif.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar kwafin takardun kudirorin daukacin kungiyoyin matasan a harabar gidan Gwamnatin Jihar Kaduna.
Kungiyoyin karkashin jagorancin shugaban gamayyar kungiyoyin Nastura Ashiru Shatif, ya mikawa kungiyar Gwamnonin irin kudirin da kowace kungiyar ta rubuta a matsayin korafi ko hasashe tare da hangen nesa a matsayin shawarwarin da suke bukatar a aiwatar domin ciyar da kasa gaba.
Indai za a iya tunawa Nijeriya ta shiga cikin wani hali ne inda kungiyoyin matasa da dama suka fita kan tituna suna zanga zangar neman samar da Gyara a bangarorin rayuwa daban – daban domin samun sahihiyar rayuwa musamman ga yan baya.
Amma wannan yunkuri na matasan ya ga mu da matsala inda wasu matasa suka mayar da lamarin kwasar ganima, kone Kone tare da Barnar dimbin Dukiya, wanda hakan ya saba da abin da yasa aka fito domin zanga zangar tun farko.
Gwamna Simon Bako Lalong wanda shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin arewa ya godewa kungiyoyin matasan karkashin jagorancin Nastura Ashiru Sharif kan yadda suka nuna halin yakamata game da zanga zangar da tun farko aka fito da niyya mai kyau, amma wasu batagari suka lalata lamarin
“Abin da ake bukata shi ne girmamawa da halin yakamata kuma a wannan tsarin hakika matasan Arewa sun nuna don haka a madadin dukkan Gwamnonin Arewa muna yi maku godiya bisa yadda kuka nuna biyayya da ladabi, kuma tuni na rigaya na mikawa Gwamnoni irin kudirinku da kuka cimma kowa ya yi murna da farin ciki game da hakan.
Kamar yadda zaku iya gani a cikin wannan hoton shugaban gamayyar kungiyoyin matasa ne Nastura Ashiru Sharif yake mikawa Shugaban kungiyar Gwamnoni takardun sauran kungiyoyin domin a mikawa Gwamnatin tarayya domin yin nazari.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.