Daga Imrana Abdullahi
Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai Mai Kula da masaukin bakin Al’ummomi kuma Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu Honarabul Malam Abdulkarim Hussaini Ahmed (Mai Kero), ya mika ta’aziyya ga Dan takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, a zaben da ya gabata a Jihar Kaduna Injiniya Hannafi Aminu da daukacin ‘yan uwa bisa rasuwar Mahaifiyar shi a ranar laraba.
Bayanin haoan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Sharifudeen Ibrahim Muhammad (Dan Jarida) Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa da aka rabawa manema labarai a Kaduna
Honarabul Hussaini Mai Kero, ya bayyana rasuwar Mahaifiyar Hannafi a matsayin babban rashi ba ga danginsu kawai ba, har ma da Jihar Kaduna da Nijeriya baki daya, inda ya ce rasuwar ta haifar da wani gibi da yanayi mai wuyar cikewa musamman ga dangi da yan uwa baki daya.
“Ta kasance uwa ta gari, wacce ta nuna soyayya da kulawa, haka nan kuma mai sadaukarwa a lokacin rayuwarta”, inji shi.
Ya yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama ya kuma baiwa iyalai, karfin gwiwar jure wannan babban rashi.