DAGA IMRANA ABDULLAHI
Shugaban hukumar tara kudin haraji na kasa Muhammad Nami ya bayyana cewa hukumar ta tara makudan kudin da suka kai naira tiriliyan Goma da kusan biyu a shekarar da ta gabata, 2022.
Hajiya Sa’adatu Yero ce ta bayyana hakan a lokacin da ta wakilcin shugaban hukumar a wajen bikin ranar hukumar tara kudin haraji ta kasa (FIRS), a kasuwar baje koli ta kasa da kasa da ke ci a halin yanzu a Kaduna.
Hajiya Sa’adatu Yero ta ci gaba da cewa wannan kokarin da hukumar ke yi duk sakamakon irin Namijin kokari ne da aiki tukuru daga ma’aikatan hukumar Masu kishin kasa da son al’ummarta baki daya.
“Domin ana yin amfani da wadannan kudin ne wajen biyan Albashi da sauran gine ginen Makarantu da asibitocin Gwamnatin tarayya domin amfanin jama’ar kasa”.
Sa’adatu Yero ta ci gaba da yin kira ga daukacin jama’ar kasa da a koda yaushe su rika biyan harajin da ya dace su biya Gwamnati a duk wuraren da suke aiki ko aiwatar da wata sana’ar da suke yi ta halaliya.
“Mu a hukumar tara kudin haraji ta kasa za mu ci gaba da aiwatar da aikin da ya dace domin samun biyan bukatar yan kasa”.
Ta ce muna kokarin shawo kan mutane ta hanyar yi masu bayanin da ya dace a koda yaushe domin su ga muhimmancin biyan kudin haraji wanda ya kasance hakki ne na kasa.
Hajiya Sa’adatu Yero ta kuma ya ba wa irin yadda masu shirya kasuwar duniya ta kasa da kasa suke kokarin shirya kasuwar a dukkan shekara, lamarin da ta bayyana da cewa abin a yaba ne domin kara bunkasa tattalin arzikin kasa ne.
Sai ta yi kira ga jama’a da su rika kokarin zuwa Ofisoshi da sauran cibiyoyin yi wa jama’a bayani ko korafi a kan dukkan abin da ya shige wa jama’a duhu, domin wanda hukumar ta yi tsare tsare masu inganci da har wadanda ke zaune a yankunan karkara za su samu damar samun waraka a kan abin da ke damuwarmu game da ayyukan hukumar.
Hajiya Sa’adatu Yero ta samu wakilcin Mista Richart da sauran wadansu manyan ma’aikata da sauran ma’aikatan hukumar da dama