Home / Labarai / Hukumar Kula Da Yan Gudun Hijira Ta Kasa Za Ta Horas Da Mutane Dubu Goma (10,000)

Hukumar Kula Da Yan Gudun Hijira Ta Kasa Za Ta Horas Da Mutane Dubu Goma (10,000)

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Hukumar kula da yan gudun hijira a tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta horas da mutane yan gudun hijira na cikin gida tare da hadin Gwiwar hukumar da ke Koyar da kimiyyar sarrafa bayanai ta kasa (NITDA) za su horas da mutane a Abuja guda dubu Goma (10,000).
Za a fara ne da mutane dari biyu a da za su halarci horon a bangaren kimiyyar zamani ta yanar Gizo, za kuma a ba su Kwamfutar hannu domin kara inganta basira da ilimin da suka samu.
Da yake gabatar da bayani, Kwamishinan hukumar kula da yan gudun hijirar wadan da aka tsugunnar, Honarabul Imaan Suleiman Ibrahim cewa ta yi tsarin horaswar zai taimaka wajen kara Sanya su hulda a cikin al’umma, ta yadda za su ci gaba da gudanar da al’amuran rayuwa kamar kowa.
A cikin wata takardar da sashen yada bayanai na hukumar ya fitar ya ce babban dalilin da ya sa za a koyawa yan gudun hijirar wannan aikin yin amfani da yanar Gizo shi ne domin su samu dama kamar sauran jama’a na jerawa da zamani kuma ya taimaka masu ta fuskar dogaro da kansu har wasu ma su ci moriyar abin daga gare su kuma su fita daga cikin matsayin da suke ciki a halin yanzu.
Hajiya Suleiman Ibrahim ta kara da cewa hukumar za ta ci gaba da aikin bunkasa ayyukan da za su inganta harkokin dogaro da kai musamman daga bangaren yan gudun hijira da komai zai dace da kokarin Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da sauran shirye shiryen bunkasa tattalin arzikin kasa musamman ga marasa karfi a cikin al’umma.
Sai ta godewa Darakta Janar na  hukumar NITDA Inuwa Kashifu Abdullahi da yake kokarin fadada ayyukan hukumarsa domin horas da wadannan mutane yan gudun hijira.
A nasa jawabin Abdullahi cewa ya yi hukumarsa an Dora mata alhakin kokarin bunkasa fasahar sadarwar zamani domin samar da bayanai a Najerita baki daya.
Da kuma dokar da ta ba su damar samar da tsarin shiryawa,bincike, binkasawa da kuma kara ingantawa a dukkan lamuran baki daya da ya hada da yin aikin hadin Gwiwa Gwiwa sauran hukumomi wajen aikin horaswa da nufin kara bunkasa ayyukan ma’aikatansu.
 A dai kokarin samun ci gaban rayuwa an yaba wa hukumar yan gudun hijirar saboda aikin horas da mutane Hamsin (50) a unguwar Jabi cikin babban birnin tarayya Abuja.
Babban aikin horaswar zai fara ne da aikin koyawa wasu aikin yin takalma, Walda,sana’ar Tela,Aikin Girke – Girke, aikin sarrafa bidiyo, aikin gyaran gashi,kirkirar dandalin shafukan tamar Gizo, sana’ar Aski da ba su kayan fara aiki bayan kammala samun horon.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.