Home / Labarai / HUKUNCIN KOTU YA TABBATAR DA ZAN IYA TSAYAWA TAKARAR GWAMNA – ISA ASHIRU

HUKUNCIN KOTU YA TABBATAR DA ZAN IYA TSAYAWA TAKARAR GWAMNA – ISA ASHIRU

IMRANA ABDULLAHI
Gabanin lokacin zaben fitar da Gwani a jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, dan takarar Gwamna Honarabul Isa Mohammd Ashiru ya bayyanawa manema labarai cewa hukuncin da babbar kotu ta yanke ta wanke shi zai iya tsayawa takarar fitar ga Gwanin.
Tsohon dan majalisar wakilai Isa Ashiru ya ce hukuncin da wata babbar kotu ta yanke kwanan nan inda ta Kori  baki daya da karar a matsayin mara tushe da aka gina a kan jiga- jita kawai cewa Isa Ashiru bashi da takardun makaranta balantana ya samu damar cika sharadin tsayawa takarar Gwamna, wanda wani dan jam’iyyar PDP mai suna Isa Abdullahi, ya kai karar.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis, daraktan kula da harkokin shari’a na kwamitin neman zaben Honarabul Isa Ashiru, Barista Husaini Abdu cewa ya yi bayan an wanke shi kuma ya cancanci tsayawa takara.
Ya ce “muna tattara sunayen wadanda suka yi wa dan takarar mu batanci da nufin daukar matakin doka sai dai in har sun yi abin da yakamata na wallafa bayanin ban hakuri a cikin manyan jaridun kasar nan masu fita a kullum da daukar matakin cewa sun yi Nadama da irin abin da suka aikata”.
Shi wanda ya shigar da kara a gaban wata babbar kotu a Zariya Isa Abdullahi cewa Honarabul Isa Ashiru bashi da takardun makaranta da zai tsaya takarar Gwamna a Jihar Kaduna don haka ya gabatarwa da kotu kararsa.
“Amma Ashiru ya gabatar da korafin kalubalantar wannan kara inda ya ce hakika ya can – can – ci tsayawa takara domin ya na da ingantattun takardu saboda haka nema ya bukaci a bashi kudi naira miliyan daya (1) domin bata masa suna.
Honarabul Isa Ashiru ya gabatar da takardun makaranta guda shida da duka hada da satifiket na kammala karatun sakandare da aka bashi a shekarar 1980 da ya kammala kwalejin Kufena, Zariya. Sai takardar karatun Difiloma ta kasa da kuma babbar Difiloma da ya kammala daga kwalejin foli, sai kuma shaidar kammala karatun PGD da shaidar kammala karatun digiri na uku a bangaren karatun gudanar da mulki daga jami’ar Bayero da ke Kano.
Kamar dai yadda Lauya Abdu, ya ce a ranar 9 ga watan Mayu 2022, alkalin babbar kotu M. K. Dabo ya kori karar baki daya.
An Kori karar ba ma wai an yi watsi da ita ba, don haka ba za a iya dawo da ita kotu ba kenan har abada sai dai idan an daukaka kara, kuma a iya sanin mu har yau ba a daukaka karar ba.
“Wanda ya yi karar ya cika wani bangare na hukuncin da aka yi da kotu ta bukaci a wallafa bayanin bayar da hakuri a jarida amma har yanzu bai wallafa na biyu ba kuma bai biya kudin da kotu ta bukata ya biya wanda yake kara ba”.
Dan takarar Gwamna Isa Mohammad Ashiru zai yi dukkan abin da ya dace domin tabbatar da an samu nasarar zaben fitar da dan takara.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.